Ƙasa da shekara 30, gwaggon-biri waɗanda ke zama a kan tsauni ba su wuce 680 ba. / Hoto: Marsden Momanyi, WWF

A shekarar 2018, na ci sa'a inda na shiga wata tawaga ta ƙungiyoyi takwas waɗanda suka kafa Shirin Ƙasa da Ƙasa na Alkinta Gwaggon-Biri.

An ba mu wani kati kyauta na yawon ganin gwaggon-birai wadda gwamnatin Rwanda ta ba mu. Katin yana kai kusan dalar Amurka 1,500 ga baƙi daga wajen Afirka, waɗanda suke kuma daga Gabashin Afirka suna biyan dala 200.

A hankali muka rinƙa tafiya yi a cikin gandun dajin don neman daya daga cikin iyalan gwaggon-birin.

Mun bi jagoranmu a hankali wanda lokaci-lokaci yakan tsaya ya gyara mana hanya tare da amfani da addarsa domin sassake bishiyoyin da suka shige mana gaba domin shiga cikin dajin na Gabashin Afirka.

Samun damar haɗuwa

A ƙarshe, mun zo ga wani ɗan ƙaramin fili mai kauri kewaye da bishiyoyi ta kowane bangare. Sai ga wasu gwaggon-birai 12 kwance suna baccin rana.

Sai dai kawai wani gwaggon-biri ɗaya tal wanda a hankali ya rinƙa tauna wasu karmami, wanda ɗan jagoran nanmu ya shaida mana cewa suna matuƙar jin daɗinsa.

Kawai sai na ji ni wani ɗan ƙarami kuma ba ni da wani amfani a gaban irin waɗannan manyan dabbobin kuma masu ƙarfi.

Sai wasu jariran gwaggon-biran suka dakatar da wasan da suke yi inda suka mayar da hankalinsu a kanmu, inda suke kallonmu wato baƙinsu cikin mamaki a daidai lokacin da muke daddana wayoyinmu domin ɗaukarsu hotuna.

Sai ɗaya daga cikin jariran ya yi rarrafe ya hau kan wani siririn reshe sannan ya sulalo da jikinsa ƙasa zuwa wurin da muke. Bayanmu daji ne babu wani wurin guduwa.

Muna sane sarai da yadda suke bayar da kariya ga 'ya'yansu, sai kowa daga cikinmu a hankali ya ja da baya har muka haɗe tare. Haka kuma, bayanmu ya kasance a jikin jerin itatuwa, babu wurin da za mu gudu.

Jariran gwaggon-birai a cikin daji. / Hoto: Marsden Momanyi, WWF

Jaririn na biyu ya bi sawu, ya sauko da ƙarfi inda hakan ya sa wata macen gwaggon-biri ta zura mana ido.

Waɗannan taƙaitaccen lokacin da aka raba tare da gwaggon-biran ba kawai tawali'u ba ne, amma tunatarwa ce ta yadda muka yi kusa da rasa waɗannan dabbobi masu ban sha'awa, waɗanda ke ɗauke da kaso 98 na ƙwayoyin halittarmu.

Farfaɗowa mai kyau

Kasa da shekaru talatin da suka wuce, akwai gwaggon-birai 680 kacal a duniya. A yau, godiya ga sadaukarwa da ƙoƙarin dawo da haɗin-gwiwa, sun kai sama da 1,000.

Wannan farfadowa ce ta ban mamaki, wadda ta farfaɗo da abin da aka rasa tsawon shekaru. Yanzu su ne kawai nau'in birai waɗanda yawansu ke kan gaba.

Duk da nasarar da aka samu, duk da haka gwaggon-birai na fuskantar ƙalubale daban-daban. / Hoto: IGCP

Sakamakon yadda ake samun ƙaruwar gwaggon-birai na kan tsauni, a 2018, IUCN ta sake sauya matsayarta daga 'waɗanda ke cikin tsananin hatsari' zuwa 'waɗanda ke cikin hatsari'.

Nasarar tana da girma kuma an same ta ne sakamakon irin haɗin-gwiwar da aka yi tsakanin al'ummomi mazauna yankin da gwaggon-biran suke.

"Mun san darajar gwaggon-birai da ke kan tsaunuka, shi ya sa muke ƙoƙarin ƙillace su da kuma tabbatar da cewa suna cikin wurin amintacce," kamar yadda Dukundimana Joseline ta bayyana wa tawagarmu, wadda wata manomiya ce daga wani ƙauye da ke kusa da gandun dajin.

"Idan masu yawon buɗe ido suka zo, kuɗin da suke biya na taimakon jama'ar ƙauyen.

Sakamakon irin kuɗaɗen da ake samu ta hanyar gwaggon-birai, an gina gidaje ga wasu jama'ar ƙauyen, a halin muna samun ruwa mai tsafta da wutar lantarki da hanyoyi," in ji ta.

"Akwai matuƙar amfani a alkinta gwaggon-birai na kan tsauni, sun cire mu daga talauci," kamar yadda ta ƙara da cewa.

Mafarki ya tabbata

"Na rinƙa jin labarai masu daɗi game da gwaggon-birai na kan tsauni, kuma ganinsu a karon farko sai na ji tamkar wani mafarkina ne ya tabbata," kamar yadda Riwe Emimah ta bayyana.

"Kudaden da ake samu daga yawon bude ido, an saka hannun jari ne wajen bunkasa ababen more rayuwa a cikin al’ummarmu. Yanzu muna da cibiyoyin kiwon lafiya a kauyukanmu kuma ba za mu yi tafiya mai nisa don samun magani ba.

"A baya, muna kashe 1,500 na Rwandan francs (kimanin dalar Amurka 1.2) a sufuri amma yanzu yana ɗaukar mu mintuna 15 kawai da ƙafa zuwa cibiyar lafiya," kamar yadda ta ƙara da cewa.

Wani mutum a cikin al'ummar, Mperanya Jean Damascene ya tabbatar da karuwar kudaden shiga daga farfado da tattalin arzikin yawon bude ido.

A baya nakan shiga wurin dajin ba bisa ka'ida ba don in samo sandunan da za su taimaka wa wake na, sau da yawa nakan fada barazanar samun rauni da kuma hari daga dabbobin dawa, sau da yawa a kan farashin kuɗin da ba su wuce 500 Rwandan francs ba.

A yau ina amfana ta hanyar yi da sayar da kayan aikin hannu da kayan fasaha. Kujera daya tana samo mani sama da Rwandan francs 15,000 (kimanin dalar Amurka 12) kuma yanzu zan iya biyan bukatun iyalina."

Ƙoƙarin alkintawa da kuma ƙalubale

Wadda aka kafa a shekarar 1991, Shirin Ƙasa da Ƙasa na Alkinta Gwaggon-Biri (IGCP) haɗin gwiwa ce ta musamman ta ƙungiyoyin alkintawa ta duniya - Conservation International, Fauna & Flora International da WWF, tare da haɗin gwiwa tare abokan tarayya na ƙasa da na gida don tabbatar da wanzuwar dajin na tsawpn lokaci wanda ke ɗauke da gwaggon-biran da ke cikin hatsari.

IGCP mallakar gida ce, kuma tana aiki tare da goyon bayan duniya, gudanarwa da bayar da shawarwari ga mafi kyawun ayyuka na yawon shakatawa da kallon gwaggon-birai.

Duk da irin nasarar da aka samu wurin alkinta gwaggon-biran na kan tsauni, har yanzu aƙai ƙalubalen da suke buƙata. Rikici tsakanin jama'a da kuma namun dawa - musamman ɓauna da giwaye da gwaggon-birai a wani lokacin - wani ƙalubale ne sosai.

Farautar gwaggon-biri na tsaunin don abinci abu ne mai wuyar gaske, amma kafa tarko don kama gada da aladun daji da sauran namun daji na kashe ko raunata gwaggon-biri na tsaunuka, wanda ke kawo illa ga rayuwar wannan nau'in.

A cikin shekarun da suka gabata, rashin kwanciyar hankali na siyasa da rikice-rikicen masu ɗauke da makamai a sassan yankin sun sanya aiwatar da doka, da sa ido kan gwaggon-birai ya zama abu mai wahala, haka kuma irin waɗannan biran suna da wahalar sabawa da sauyin yanayi.

Matsugunan mutane suna takura musu yiwuwar tarwatsewa, kuma suna fuskantar gazawa saboda ƙarancin bambancin halittarsu da ƙarancin haihuwa da jinkirin haihuwa.

Marubucin Marsden Momanyi, shi ne shugaban watsa labarai na ƙungiyar The World Wide Fund for Nature, WWF, wadda ita ce ƙungiyar da ke kan gaba wurin alkinta dabbobin da ke cikin hatsari.

Togaciya: Ba dole ba ne ra'ayin marubucin ya yi daidai da ra'ayi ko ka'idojin aikin jarida na TRT Afrika ba.

TRT Afrika