Eswatini ranks among the top 10 African countries with the highest suicide cases. Photo: Getty Images

Daga Bonisile Makhubu

Kowa yana da muhimmanci idan ana maganar kashe kai: daidaikun mutane da dangi da abokai da abokan aiki da al'umma da malaman makaranta da malaman addini da kuma 'yan siyasa. Mutane da ke daukar ran kansu a kowace rana, kuma ya kamata ne a yi maganin matsalar kashe kai a kowace rana.

Matakin farko shi ne 'fara daga kanka'. Ya dace mutane su fara fahimtar cewa suna bukatar taimako kuma su dauki matakin da ya dace.

Ranar Yaki da Kashe Kai rana ce daya tilo da ya kamata a tashi tsaye wajen wayar da kan jama'a kan matsalar kashe kai, wanda hakan shi ainihin kashe kai ko kuma yunkurin kashe kai.

Abin a yaba ne cewa yayin bikin na bana Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta samar da duka abubuwan da ake bukata wajen yaki da matsalar kashe kai, wadanda za su taimaka wa daidaikun mutane da suke fuskantar kalubalen rayuwa.

Sabbin tsare-tsaren yaki da matsalar kashe kai suna da muhimmanci ga kasashen Afirka, inda ake ci gaba da samun karuwar mutanen da ke kashe kansu, adadin ya fi tsaka-tsakin adadin duniya, inda ake samun mutum tara suke daukar ransu cikin mutum 100,000 a kowace shekara.

Wasu kasashe sun sanya a dokokinsu cewa harum ne mutum ya kashe kansa ko kuma ya yi yunkurin kashe kansa. Wannan ya sa yaki da matsalar kashe kai take da wahala kuma hakan ya kara nisanta nahiyar daga cimma Muradu Masu Dorewa na Majalisar Dinkin Duniya (SDGs), ana fatan rage adadin masu kashe kansu a duniya da kaso daya bisa uku daga nan zuwa shekarar 2030.

National Psychiatric Referral Hospital

Eswatini tana cikin kasashen, masarauta ce a yankin Kudancin Afirka, wacce mutanenta miliyan 1.2 suke fuskantar matsalar barazanar kashe kai saboda dalilai iri daban-daban ciki har da tarihinsu da lafiyar kwakwalwa da salon tafiyar da rayuwa da dabi'u da matsalolin da suka jibanci wajen aiki da zamantakewa.

Matasa

An saka wannan kasa a cikin jerin kasashe 10 da mutane suka fi kashe kansu. A rahoton, Bankin Duniya ya ce kasar Eswatini ita ce ta biyu bayan Lesotho a nahiyar. Kasashen biyu suna da adadin mutane da ke kashe kansu 72.4 da 29.4 cikin kowane mutum 100,000 kowace. Babbar tambayar ita ce me ya sa?

Eswatini kasa ce da aka bari a baya wajen magance matsalolin lafiyar kwakwalwa da samar da dokoki. Yayin da a yawancin kasashe, ana kallon matsalar kwakwalwa da wani nau'in cuta, a Eswatini ana kallon mutanen da suka kashe kansu ko suka yi yunkurin kashe kansu da manyan masu laifi maimakon mutanen da ke bukatar taimako.

Dalibai da dama ba sa neman taimako idan suna cikin matsalar kudi a jami'a ko babbar makaranta. Madadin haka zai su zabi su kashe kansu.

A shekarar 2022, kusan dalibai 40 da suka daina zuwa makaranta a Eswatini sun yi yunkurin kashe kansu saboda sun kasa biyan kudin makarantarsu.

A baya-bayan nan daraktan wata kungiya mai suna Swatini Action Against Abuse, SWAGAA, Nonhlanhla Dlamini, ya ce kafafen sada zumunta sun sa matasa suna son yin rayuwar karya.

Saboda tasirinsu, hakan yakan sa matasa da dama yin amfani da su a matsayin ma'aunin nasara a rayuwa.

A van used to ferry non-violent mental health patients is packed outside the National Psychiatric Referral Hospital. Photo: TRT Afrika

Cin zarafi yana daya daga cikin manyan abubuwan da ke jawo kashe kai a tsakanin mata matasa wadanda ba sa kawo rahoton cin zarafin da aka yi musu saboda tsangwama.

Wani nazari da aka yi kan cin zarafin yara da matasa Violence Against Children and Youth Survey (VACS) da aka yi a shekarar 2022 ya ce ba kasafai ake daukar mataki ba, idan aka kawo rahoton cin zarafi.

Alkawarin da Hukumar WHO ta yi shi ne "samar da tsari ta yadda doka za ta daina kallon wadanda suka kashe kansu ko yunkurin haka a matsayin masu laifi saboda hakan zai rage tsangwamar da suke fuskanta kuma zai samar da yanayi da zai sa mutane neman taimako; hakan zai samar da ingantattun bayanai kan kashe kai da yunkurin kashe kai wanda zai samar da magance matsalar; kuma ya samar da damar wayar da kai da kiraye-kirayen dakile matsalar kashe kai."

Rawar da kafafen yada labarai za su iya takawa

Kasar, da gaba daya nahiyar Afirka za su iya cin moriyar wannan tsari da magance tsaiko, daya daga ciki shi ne dokar kashe kai ta Homicide Act ta 1959 ta Eswatini, sashi na 4, wacce take kallon kashe kai a matsayin babban laifi.

Hujjar ita ce doka ce da ba a aiwatar da ita, tun da wanda ya aikata laifin ya rigaya ya mutu, amma 'yan sanda sun kafe cewa dokar tana nan ne don a yi aiki da ita.

Galibin mutanen da suka kashe kansu sun sha yin yunkurin kashe kansu a baya sau daya ko ma fiye da sau daya, in ji masana.

Jami'in Hukumar WHO Nathalie Drew Bold yana ganin yin dokar wadda take kallon kashe kai a matsayin babbar laifi kara dagula wa mutane tsananin damuwar da suke ciki ne. Ya bayar da shawarar cewa ya kamata gwamnati ta dauki matakin doka na daina kallon kashe kai ko yunkurin yin haka a matsayin babban laifi.

Kafafen yada labarai suna wayar da kan jama'a da ilmantar da su da kuma yada bayanai, kuma ya kamata su rike rawar da za su iya takawa da muhimmanci.

Sannan su wayar da kan jama'a kan su rika yin magana idan suna da matsaloli, kuma su samu mutanen da za su rika fada wa matsalolinsu, kuma ya dace dangi da abokin arziki da su dauki barazanar ko yunkurin kashe kai da muhimmanci sosai.

"Manyan kafafen yada labarai za su iya taimaka wa wajen samar da ingantattun da sahihan rahotanni kan matsalar kashe kai da kuma karfafa mutane gwiwa kan muhimmancin neman taimako," in ji Dokta Alexandra Fleischmann, masanin kimiyya da ke aiki da Hukumar WHO.

Marubucin Bonisile Makhubu dan jarida ne da ke zaune a Eswatini.

Togajiya: Mahangar da marubucin ya bayyana a nan ba sa wakiltar ra'ayoyi da mahangar iditocin TRT Afrika ba.

TRT Afrika