Cututtukan kasashe masu zafi da aka yi biris  da su  (NTDs) na shafar mutane biliyan 1.6 a kowacce shekara. Hoto: DNDi

Daga Collins Mutua

Shin kun taba tunanin ta yaya kwayoyin magungunan da ke gidajenku suke isa gare ku?

Ana bukatar rukunin mutane kafin a samar da magunguna. Wadannan mutane sun hada da masu bincike, ma'aikatan asibiti, masu sadaukar da kai don gwada magani, mahukunta da masu rarraba magungunan.

Kamfanonin samar da magunguna na bin hanyoyi masu wahala na gwaji da gano sabbin magunguna tare da auna ingancinsu ga dan'adam a dakunan bincike da gwaje-gwaje, kafin a gwada su a kan 'yan'adam.

Da zarar an tabbatar da inganci da tabbaci wajen gwaji kan mutane, sai hukumomi su yi nazari kan sakamakon da aka samu tare da bayar da izinin fara samar da magungunan don sayar da su.

Daga nan sai a fara sanya idanu kan magunguna yayin tallata su, don tabbatar da tsaro da ingancinsu.

Sai dai kuma, jaruman da ke taka rawa wajen samar da magani amma ba a ganin su, su ne masu kula da bayanai da masana kididdiga.

Cututtukan da aka yi biris da su

Misali, a 2003, wasu masana kimiyya daga Sudan, Uganda, Kenya da Ethiopia sun hada gwiwa wajen gano tsayayyen maganin cutar da aka fi sani da 'visceral leishmaniasis' ko kala-azar.

Maganin da ake da shi a yanzu shi ne alluran kwanaki 30, wadanda suke da tsada kuma a mafi yawancin lokuta suke da illa.

Wasu masana kididdiga, kwararru kan sarrafa bayanai da masu shirye-shirye ne suka samar da tsayayyun bayanan lafiya don taimaka wa masana kimiyyar.

Masana kididdigar sun samar da hanyar gwaji don tabbatar da cewa binciken ya dace da kimiyya, kuma maganin yana da tasirin da ake fatan samu.

Masu kula da bayanan sun samar da wata ma'ajiyar bayanai, don su tabbatar da bayanan da ake bukata a tattara sun cika, tsaftatattu kuma ba sa dauke da wani kuskure a yayin da aka aika su zuwa ga ma'ajiyar tasu.

Masu shirya ayyukan sarrafa bayanan kuma suna shirya bayanan don fara nazari a kansu, daga baya kuma masana kididdiga su yi filla-filla da su don tabbatar da kyau da ingancin magungunan, su fassara sakamakon da aka samu, tare da rubuta rahoto.

Kula da lafiya mafi inganci

Bayan shekaru bakwai, a watan Maris na 2010, Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta amince da bayar da shawarar amfani da wannan sabon magani, wanda ya fi karko da tasiri, kuma mara lafiya na amfani da shi na tsawon kwanaki 17.

Maganin ya yi tasiri sosai ga rayuwar dubban masu fama da cutar 'visceral leishmaniasis' a Gabashin Afirka, wadanda rabin su mata ne da yara kanana da suka fito daga al'ummun da talauci ya yi wa katutu.

Wannan bajinta da masu kididdiga suka yi ta sa an samar da sabon tsarin kula da lafiya ga wannan cuta da a baya aka yi biris da ita.

Cututtukan kasashe masu zafi da aka yi biris da su (NTDs) na kama mutane biliyan 1.6 a kowacce shekara, kuma Afirka na dauke da kashi arba'in na adadin masu dauke da cutar a duniya. A kasata Kenya, sama da mutane miliyan 25 na dauke da 15 daga cikin 20 na cututtukan da aka yi biris da su.

Abin takaici, ga mutane da yawa, maganin da ake amfani da shi a yanzu ba ya yi musu aiki, wasu na da karancin warkewa daga cuta ko samun illa bayan amfani da magani, wanda ka iya janyo rasa rai.

Manyan kamfanonin hada magunguna ba su cika mayar da hankula kan irin wadannan magunanan gargajiya ba saboda ba sa samar da gwaggwabar riba.

Kamfanunnukan magunguna na yin gwaje-gwaje sosai don gano sabbin magunguna.Hoto: DNDi

Kalubale

Ina alfaharin zama daya daga cikin masana kididdiga da suka bayar da gudunmawa wajen samar da magani mafi inganci na cutar kala-azar a Gabashin Afirka.

Tun bayan kafa Hukumarmu a 2004 karkashin wata kungiyar binciken samar da magunguna mai suna 'Samar da Magungunan cututtukan Da Aka Yi Biris Da Su (DNDi)', mun taimaka wajen yin gwaje-gwaje kan marasa lafiya a asibitoci da dama don gano wadannan cututtuka.

Ba wai da DNDi kawai muke aiki a Afirka ba, har ma da sauran kungiyoyi da suka hada da WHO, Kungiyar Likitocin Komai da Ruwanka da Cibiyar Binciken Magunguna ta Kenya (KEMRI).

Tallafin da muke bayarwa wajen gwajin magunguna a kan mutane na wasu cututtuka, kamar tarin fuka da ke bijire wa magunguna, ciwon ulcer na Buruli, ya bayar da gudunmawa sosai wajen ci-gaban kula da cututtuka.

A baya-bayan nan, mun yi wani aiki a Sudan kan sabuwar hanyar magance cutar 'mycetoma', cutar da ke janyo nakasu da dama a jikin dan'adam. Muna fatan bincikenmu zai kai ga samar da magunguna ga masu fama da wannan mummunar cuta.

Kwararan bincike

Sai dai kuma, aiki kan cututtukan da aka yi biris da su na zuwa da kalubale da dama.

Na farko dai, sabon rashin bayar da kulawa ga wadannan cututtuka, ana fuskantar rashin isassun bayanai da za a gano adadin da ake bukata don jarraba magani.

Wannan adadi ya samu ne duba da bayanan bincike da ake da su, wand aba shi da yawa game da wadannan cututtuka. A irin wannan yanayi, ana iya bukatar wasu hanyoyi na daban don yin bincike, wanda suna daukar lokaci mai tsawo.

Masu bincike na bukatar karin zuba jari a binciken likitanci game da cututtukan da aka yi biris da su, kuma wannan zai kai ga samar da karin hanyoyi sabbi na magance wadannan cututtuka.

Gwaji kan sabbin hanyoyin kula da lafiya na iya samar da sakamakon mafi kyau, idan aka gudanar da shi a wurare daban-daban.

Hakan ya sanya muke bukatar gwaji kan marasa lafiya da kuma cibiyoyin adana alkaluma a yankuna don gujewa zuwa kasashen waje wand ake daukar tsawon lokaci kafin sakamakonsu ya dawo.

Kalubale na biyu kuma shi ne rashin kayan aiki, kamar hanyoyi, yanar gizo, wanda har yanzu suke janyo wahala wajen gudanar da gwaji kan mutane a yankuna masu nisa.

Domin magance wani bangare na wannan kalubale, muna amfani da tsarin tattara bayanai na zamani da ake iya ba tare da amfani da yanar gizo ba, wanda ke bayar da dama mu tattara bayanai kai tsaye daga inda marasa lafiya suke, a kuma tura su zuwa ma'ajiyar bayanai nan take ba tare d ayanar gizo ba.

Ya kamata gwamnatocin Afirka su bayar da muhimmanci ga cigaban kayan more rayuwa don samun damar tabbatar da cibiyoyi a yankuna da z asu karfafa hadin kan Kudu Maso-Kudu.

A karshe, wasu kasashen na da tsauraran dokoki game da bayanai. A yayin da yake da muhimmanci a girmama kare dokokin bayanai, yana kuma da muhimmanci a nemo hanyoyin da za a dinga tattara bayanan marasa lafiyan da ba a bayyana su waye ba, kuma daga kasashen duniya da dama, wanda hakan zai kara yawa bayanan da inganta bincike.

Ya zama dole Afirka da sauran yankunan duniya su yi alfahari da kokarin da kwararru kan kididdiga ke yi, musamman yadda suke bayar da gudunmowa ga yaki da cututtukan da aka yi biris da su.

Ci gaba da bayar da sakamakon binciken lafiya matabbaci na da muhimmanci wajen samar da kimiyya mafi kyau ga cututtukan da aka yi biris da su.

Collins Mutua, shi ne Shugaban Sashen Kididdigar Dan'Adam a Cibiyar Magungunan Cututtukan Da Aka Yi Biris Da Su. (DNDi).

Hattara Dai: Ra'ayoyin da mawallafiyar ta bayyana ba dole ba ne ya dace da ra'ayoyi hange da kuma manufofin tace labarai na TRT AFRIKA.

TRT Afrika