Xavi ya amince ya ci gaba da horar da Barcelona har zuwa shekarar 2025. / Hoto: AA

Duk da matsalar kuɗi da kulob ɗin Barcelona ke fama da ita, shugaban ƙungiyar Joan Laporta ya yi wasu manyan alƙawura ga koci Xavi Hernandez don ya ci gaba da horar da ƙungiyar, bayan da a watannin baya ya ayyana aniyarsa ta barin su a ƙarshen kakar bana.

A watan Janairun da ya gabata ne Xavi, ɗan shekara 44, wanda gwarzon tsohon ɗan wasan ƙungiyar ne, ya ayyana ƙudurinsa na barin Barca, bayan wani wasa da Villareal ta doke su da ci 5-3.

Sai dai bayan wata doguwar tattaunawa da shugaban ƙungiyar Juan Laporta, da sauran mambobin kwamitin zartarwar ƙungiyar ranar Laraba, Xavi ya amince ya ci gaba da riƙe ƙungiyar har zuwa shekarar 2025.

Shafin Goal ya ambato mujallar Sport.es kan cewa tattaunawar tsakanin Xavi da shugabannin kulob ɗin, ta mayar da hankali ne kan warware duk wata rashin fahimtar juna tsakanin tawagar mai horar da kulob ɗin, da shuwagabannin kulob ɗin.

A tattaunar ne ɓangarorin biyu suka feɗe biri har wutsiya kan burikansu, don tabbatar da kyakkyawar alaƙa da za ta haifar da ɗa mai ido ga kulob ɗin a nan gaba.

A ƙarshe, sun amince tsakaninsu kan cewa Barcelona na buƙatar ƙarfafa tawagarta don ta iya gogayya da ƙwazo a kaka mai zuwa.

Fannoni da suke buƙatar ƙarfafawa su ne 'yan wasan tsakiya, musammam nemo gwanin ɗan wasan da zai iya take ƙwallon da za a iya kai hari. Sai kuma samo haziƙin ɗan wasan gaba ta gefen hagu.

Baya ga waɗannan manyan ɓangarori, kulob ɗin na buƙatar ƙarfafa 'yan wasan baya a dama da hagu, ganin cewa Joao Cancelo, wanda aka aro daga Manchester City shi kaɗai ne ɗan wasan baya mai kyau a tawagar tasu a yanzu.

Gabanin amincewa da cigaba da zama a Barcelona a matsayin babban koci, Xavi ya nemi tabbaci game da shirin kulob ɗin game da kasuwar 'yan wasa da za a buɗe nan gaba, a cewar rahoton.

Duk da ƙarancin kuɗin da Barca ke fama da shi, Xavi ya samu kyakkyawan tabbaci daga shugabannin, dangane da manyan 'yan wasa da za a sayo a bazara mai zuwa.

Sai dai duk da haka, cimma waɗannan buruka sun ta'allaƙa ne kan wasu sharuɗa, cikinsu har da nasarar sayar da wasu 'yan wasan don samun rarar kuɗin sayo wasu.

Haka nan kuma, an ruwaito cewa Laporta yana ƙoƙarin duba yiwuwar sake lissafin kwantiraginsu da kamfanin Nike, wanda ke samar wa Barcelona kayayyakin ƙwallo. Yana fatan samun ƙarin kuɗin shiga daga kwantiragin.

Sauya matsayar da Xavi ya yi game da barin kulob ɗin, wani babban cigaba ne da zai kawo ɗorewa ga Barcelona mai tarihin nasarori masu yawan a shekarun baya.

A yanzu Barcelona za ta mayar da hankali ne kan kakar baɗi, sakamakon cewa kusan kakar bana ta ƙare, yayin da Real Madrid ke kangaba da tazarar maki 11 a gasar La Liga, inda suke neman maki bakwai kacal cikin wasanni shida da suka rage.

TRT Afrika