Hukumar kwallon kafa ta Turai ta fitar da bayanai game da irin kudin da kungiyoyin da ke taka leda a Gasar Firimiya ke kashewa kan wakilan ‘yan wasa, haka kuma akwai wasu alkaluma na ban mamaki a wadannan bayanan. Shafin Goal.
com da ke bayar da bayanai kan wasanni ya bayyana cewa a kaka biyu da suka gabata, kungiyoyin kwallon kafa na Ingila sun kashe kudi fiye da sauran na kasashen Turai.
Ga dai jerin kungiyoyin Ingila 12 da suka fi kashe kudi kan wakilan ‘yan wasa tun daga Fabrairun 2022:
1 Manchester City £51,563,571
2 Chelsea £43,160,072
3 Liverpool £33,691,782
4 Manchester United £24,726,374
5 Arsenal £16,749,072
6 Tottenham Hotspur £16,137,103
7 Aston Villa £15,623,203
8 Leeds United £15,310,814
9 Everton £13,542,845
10 West Ham United £12,030,438
11 Newcastle United £10,784,029
12 Leicester City £10,282,967
Wane ne wakilin dan wasa a kwallon kafa?
Wakilin dan wasa wanda aka fi sani da ‘agent’ wakili ne ko kuma mai shiga tsakani wanda yake kare muradun dan wasa ko kuma ‘yan wasa.
Wasu daga cikin manyan ayyukan wakilin dan wasa sun hada da tattaunawa, ciniki da kuma kulla yarjejeniya domin tabbatar da cewa wanda yake wakilta ko kuma dan wasa ya samu kwantiragi mai tsoka.
Haka kuma wakilin dan wasa yana mayar da hankali wurin samo tallace-tallace masu tsoka daga kamfanoni da daukar nauyi ga dan wasa.
Wakilin dan wasa ne ke zama tsani tsakanin ‘yan jarida da dan wasa inda shi ke shirya hira da tattaunawa.
A wani lokacin, mahaifi ko wani dan uwa na jini kan iya zama wakilin dan wasa musamman ga ‘yan wasa masu tasowa.