Tehran Sojoji dauke da makarar mrigayi Shugaban Iran Ebrahm Raisi da filin jiragen sama na Mehrabad da ke Tehran, Iran. / Hoto: Reuters

Dubban mutane ne suka taru a kan titunan Tehran babban birnin Iran don halartar jana'izar Shugaba Ebrahim Raisi da 'yan tawagarsa, waɗanda suka mutu a hatsarin helikwafta.

A ranar Larabar nan a tsakiyar birnin, mutane sun yi cincirindo ɗauke da hotunan Raisi a jikin alluna a kusa da Jami'ar Tehran, inda Ali Khamenei, shugaban addini na Iran zai jagoranci Sallar Jana'izar Raisi da 'yan tawagarsa da suka haɗa da Ministan Harkokin Waje Hossein Amirabdollahian.

A ranar Lahadi ne jirgin helikwafta da Raisi ke ciki ya yi hatsari a wani yanki mai tsaunuka da hazo ya baibaye da ke arewacin Iran a kan hanyarsu ta zuwa Tebriz, bayan halartar ƙaddamar da wata madatsar ruwa a kan iyakar Azerbaijan.

Ƙasar Turkiyya na cikin waɗanda suka taimaka wajen gano jirgin da ya faɗi, kamar yadda tashar talabijin ta ƙasar ta bayyana.

Kafin mutuwarsa, ana kallon Raisi, mai shekara 63, a matsayin wanda zai gaji Khamenei a muƙamin shugaban addini na Iran.

An aike wa da al'ummar birnin Tehran saƙonni ta wayar salula da ke kira a gare su da su halarci taron Jana'izar.

Manyan jami'an ƙasashen waje na halartar taron jana'izar.

Za a binne shi a Shahidai

A ranar Talata aka fara shirin jana’izar marigayi shugaban ƙasar da ‘yan tawagarsa a garin Tebriz inda dubban mutane sanye da baƙaƙen tufafi suka halarci cibiyar Qom ta babban Malamin Shi'a don yi wa marigayin addu'o'i.

Daga Tehran, za a kai gawawwakin zuwa lardin Khorasan ta Kudu, daga nan kuma a kai Raisi garinsu na Mashhad don binne shi a yammacin Alhamis.

Khamenei ya ayyana kwanaki biyar na zaman makoki a faɗin ƙasar Iran kuma ya naɗa mataimakin shugaban ƙasa Mohammed Mokhber, mai shekara 68 a matsayin shugaban riƙon ƙwarya.

TRT World