Hotunan wurin da  jirgin helikwaftan da ya ɗauko Ebrahim Raisi ya tarwatse inda ya fado kan wani tsauni da ke yankin Varzaghan/ Hoto: REUTERS  

Babban hafsan hafsoshin sojin ƙasar Iran ya fitar da rahoton farko na bincike game da hatsarin helikwaftan da ke ɗauke da shugaban ƙasar Ebrahim Raisi da ministan harkokin waje Hossein Amir Abdollahian da muƙarrabansu.

Rahoton ya bayyana cewa, an tattaro bayanai na fasaha da kuma na binciken da suka shafi hatsarin, tare da tantance wasu bayanai da ke buƙatar ƙarin lokaci don saƙe tantance su, a cewar bayanan da kamfanin dillancin labarai na Iran IRNA ya ruwaito ranar Alhamis.

Game da binciken farko da aka gudanar, an gano cewa jirgin helikwaftan yana kan hanyar da aka tsara masa bai sauya zuwa wata ba, sannan matuƙin jirgin ya yi magana da sauran matuƙan jiragen helikwaftan da ke biye da shi kimanin minti ɗaya da rabi kafin afkuwar haɗarin.

Rahoton ya nuna cewa, ba a samu wani harbin bindiga ko makamancin hakan ba a tarkacen jirgin kana jirgin ya kama da wuta ne bayan haɗarin.

Yankin da haɗarin ya auku yana da sanyi sosai da hazo lamarin da ya yi sanadin tsawaita aikin bincike da ceto har sai da safe ne kawai aka iya kaiwa wurin.

Babu wata alama ta tuhuma

Rahoton ya bayyana cewa ba a samu wani yanayi na tuhuma ba a cikin hanyoyin sadarwar na ma'aikatan jirgin.

Za a bayyana sakamakon ƙarshe na binciken da zarar an kammala.

A ranar 19 ga watan Mayu ne Shugaba Raisi ya halarci bikin ƙaddamar da madatsar ruwa a kan iyakar Iran da Azerbaijan.

A hanyar dawowarsa tare da ministan harkokin wajen ƙasar Amir-Abdollahian da wasu manyan jami'ai, jirgin saman helikwaftan da ke ɗauke da su ya faɗo.

Bisa buƙatar Iran, Turkiyya ta sanya wani jirgin samanta mara matuƙi AKINCI (UAV) ya gudanar da aikin bincike da ceto, an kuma bayyana hotunan ragowar tarkacen na binciken da jirgin saman Turkiyya ya gano ga hukumomin Iran.

Tawagar Iran ta isa wurin da haɗarin ya auku kuma sun ba da rahoton cewa babu wanda ya tsira.

Duɓɓan daruruwan mutane ne suka halarci taron jana'izar marigayi shugaban ƙasar Iran Ebrahim Raisi a birnin Mashad.

Khamenei ya jagoranci jana'izar

An yi jana'izar Raisi ne a ranar Alhamis, wadda ta samu halartar ɗimbin jama'a, kamar yadda kafafen yaɗa labarai na ƙasar suka ruwaito.

Dubban mutane ne suka yi tattaki zuwa garinsa da ke Mashhad a ranar Alhamis domin yin bankwana da Raisi gabanin binne shi bayan jerin gwanon da aka yi a garuruwan Tabriz da Qom da Tehran da kuma Birjand.

A ranar Larabar da ta wuce ne Jagoran Addinin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jagoranci addu'o'i a wajen zaman makokin bankwana da Raisi da muƙarrabansa.

AA