Yankin da girgizar kasar ta auku ya kai nisan kilomita 18 (mil 11) daga kudu da birnin Hualien

Akalla mutane hudu ne suka mutu bayan wata girgizar kasa mai karfin maki 7.4 da ta auku a gabar tekun gabashin Taiwan da safiyar ranar Laraba.

Kimanin mutane 56 ne suka samu raunuka yayin da ake ci gaba da aikin ceto bayan afkuwar girgizar kasar.

Girgizar kasar ita ce mafi girma da ta afku a tsibirin a cikin shekaru 25. Kimanin mutane 2,400 ne suka mutu a shekarar 1999 lokacin da wata girgizar kasa mai karfin maki 7.7 ta afku a Taiwan a tsakiyar dare.

Shugaba Tsai Ing-wen ta ba da umarnin a jibge sojoji a fadin yankunan da lamarin ya shafa.

"Rundunar sojin kasa za ta biya bukatun kananan hukumomi tare da ba da tallafi don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin 'yan kasa," in ji Tsai a wata sanarwa da ta fitar a shafinta na Facebook.

Wani jami'in ofishin shugaban kasar ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu ta wayar tarho cewa har yanzu gwamnati na kan tattara cikakkun bayanai game da "yanayin da ke kara girma."

Hukumar binciken yanayin kasa ta Amurka (USGS) ta sanar da cewa, wurin da girgizar kasar ta ta auku ya kai nisan kilomita 18 (mil 11) daga kudu da birnin Hualien.

“Baya ga asarar rayuka da barna da aka fuskanta, tasirin iftila'in ba zai wuce (misali) wasu yan wurare ba.’’ In ji hukumar

Ko da yake hukumar kula da yanayi ta Taiwan CWA ta ce girgizar kasar ta kai maki 7.2, tana mai cewa ta afku ne a gabar tekun birnin Hualien da ke gabashin Taiwan da misalin karfe 7:58 na safiyar ranar Laraba (23:58 GMT na ranarTalata).

Wasu faifan bidiyo da kafafen yada labarai na kasar suka fitar sun nuna cewa wasu gine-gine a birnin sun ruguje sakamakon girgizar kasar da ta afku wanda zurfinsa ya kai kilomita 34.8 (mil 21).

Gargadi kan mahaukaciyar guguwa ta Tsunami

Hukumar CWA ta kuma yi gargadin afkuwar mahaukaciyar guguwa mai tafe da ruwan sama ta tsunami a yankunan arewacin tsibirin kasar bayan iftila’in girgizar kasar, wanda ya haddasa zabtarewar kasa.

Lamarin ya shafi hanyoyin ababen hawa a Taipei babban birnin kasar da yankunan Taichung da Kaohsiung, yayin da jama'ar yankunan gabar teku suka soma shirin barin wurin saboda fargabar guguwar ambaliyar ruwan.

An dakatar da makarantu a yankunan da lamarin ya shafa, kazalika lamarin ya shafi wutar lantarki a yankuna da dama.

Akwai yiwuwar sake aukuwar girgizar kasar a cikin 'yan kwanaki masu zuwa.

A cewar Nikkei Asia, kamfanonin fasaha na Taiwan "na rige-rigen tantance tasirin munin lamarin."

Duk wani tasiri da girgizar kasa ta haifar a bangaren fasaha na iya haifar da cikas a yanayin aiyukan fannin fasaha.

Girgizar kasar ta ingiza kananan mabaliyar Tsunami wadanda suka kai har kudu maso yammacin kasar Japan, wanda a yanzu haka ya haifar da fargabar samun ambaliyar masu yawa.

"An fuskanci karamin guguwar ambaliyar Tsunami a tsibiran Yonaguni da Ishigaki da Miyako a yankin Okinawa," in ji hukumar kula da yanayi ta kasar Japan, tana mai gargadi kan yiwuwar afkuwar tsunamin mai girma.

Fargaban Maƙwabta

China ta ce ta damu matuka bayan girgizar kasar da ta auku.

Mai magana da yawun China a ofishin kula da harkokin Taiwan na majalisar gudanarwar kasar Zhu Fenglian, ta isar da "ta'aziyya ga 'yan uwan wadanda iftila’in ya rusta da su a Taiwan."

"Za mu mai da hankali sosai kan bala'in da kuma abubuwan da suka biyo baya kana a shirye muke mu ba da agaji." In ji Zhu

A halin da ake ciki, Cibiyar Nazarin kan aman wuta da ilimin girgizar kasa "Volcanology and Seismology" ta Philippines ta yi gargadin afkuwar mahaukaciyar guguwa mai tafe da ruwan sama ta tsunami a yankuna hudu a arewacin Luzon bayan aukuwar girgizar kasar.

An sanar da mutanen da ke rukunin tsibirin Batanes da Cagayan da Ilocos Norte da kuma Isabela game da yiwuwar afkuwar ambaliyar Tsunami tare da ba su umarnin ficewa zuwa wuraren da ke da tsaro.

TRT World