Sojojin Isra'ila da suke kutsawa yankin sun shaida wa Falasdinawa a arewacin kasar cewa su koma kudancin yankin da ke gaɓar teku.

1510 GMTMDD na hada kai da Isra'ila wajen tursasa wa mazauna Gaza ficewa daga garinsu: Hamas

Hamas ta zargi hukumar Majalisar Dinkin Duniya da ke kula da 'yan gudun hijirar Falasdinu da " hada kai" da Isra'ila a "tursasawa al'ummar Gaza barin yankinsu."

Shugaban ofishin yada labarai na Hamas Salama Maruf a ranar Laraba ya bayyana cewa alhakin wannan bala'in na jinkan ya rataya ne a wuyan hukumar UNRWA da jami'anta, musamman abin da ke faruwa ga mazauna yankin Gaza (cikin birnin) da kuma arewacinta" wadanda ke bin umarnin ficewa da aka ba su.

Sojojin Isra'ila da suke kutsawa yankin sun shaida wa Falasdinawa a arewacin kasar cewa su koma kudancin yankin da ke gaɓar teku.

Mai magana da yawun hukumar ta UNRWA bai mayar da martani nan take ba lokacin da kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya tuntube shi game da zargin Hamas

1309 GMT — Qatar na shiga tsakani a rikicin isra'ila da Hamas don ganin an saki wasu fursunpnin yaki 10 zuwa 15 da ake rike da su a Gaza don neman a tsagaita wuta na wani dan lokaci, in ji wata majiya da ta tattauna da AFP a ranar Larabar nan.

Majiyar da ta nemi a boye sunanta ta bayyana cewa "Shiga tsakanin da Qatar ke yi da Amurka na kokarin ganin an saki wasu fursunonin yaki 10 zuwa 15 a madadin tsagaita wuta na kwanaki biyu."

Masarautar ta yankin Gulf ta kasance mai goyon bayan manufofin Falasdinawa kuma tana tattaunawa sosai da Hamas.

Qatar ta kuma karbi bakuncin reshen siyasa na hamas inda nan ne wajen zaman shugaban Hamas da ya gudu Isma'il Haniyeh.

1305 GMT — Jiragen yakin Isra’ila sun kashe Falasdinawa 18

Akalla Falasdinawa 18 Isra’ila ta kashe a yayin da jiragen yakinta suka kai hari a wani gida da ke Zirin Gaza a ranar Laraba, kamar yadda ministan harkokin cikin gida na Falasdinu ya bayyana.

Jiragen yakin sun kai hari a gidan wanda yake a sansanin ‘yan gudun hijirah da ke Nuseirat, in ji ma’aikatar a sanarwar da ta fitar.

Wadanda suka shaida lamarin sun tabbatar da cewa harin da Isra’ilar ta kai ya jawo barna matuka.

1125 GMT — Adadin wadanda Isra'ila ta kashe a Gaza ya karu

Ma’aikatar Lafiya ta Falasdinu da ke Gaza ta bayar da rahoton cewa adadin mutanen da suka rasu sakamakon hare-haren Isra’ila sun kai 10,569, daga ciki har da yara 4,324.

Rahoton ya kuma bayyana cewa mutum 2,823 cikin wadanda aka kashe mata ne.

Masu makoki na addu'a a kusa da gawarwakin Falasdinawa na iyalan Daher, wadanda harin da Isra'ila ta kai ya kashe, a asibitin Indonesia da ke arewacin Gaza. Hoto/Reuters

Sama da Falasdinawa 2,550 na karkashin baraguzai na gidajen da aka lalata, daga ciki har da yara 1,350, kamar yadda ma’aikatar lafiyar ta bayyana.

0940 GMT — WHO ta saki rahoto kan adadin mutanen da Isra’ila ta kashe a asibiti

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta saki wani rahoto inda ta tabbatar da cewa hare-haren da Isra’ila ta kai asibitoci a Falasdinu da ta mamaye ya yi sanadin mutuwar mutum 509, daga ciki har da marasa lafiya, da kuma raunata mutum 447.

Isra’ilar ta kai hare-hare 229 a asibitoci da wuraren lafiya a Zirin Gaza da Gabar Yamma da Kogin Jordan tun daga watan Oktoba, kamar yadda WHO din ta tabbatar.

Ko a watan na Oktoba sai da Isra'ilar ta kai hari kan motocin da ke dauke da marasa lafiya a Gaza. Hoto/Reuters

Hukumar ta ce a Gaza kadai, sau 102 ana kai wa asibitoci hari har zuwa biyar ga watan Nuwamba.

0855 GMT — Iraki ta ba asibitocin Gaza kyautar lita miliyan 10 ta fetur

Gwamnatin Iraki ta bayar da kyautar lita miliyan goma domin amfanin janaretoci a asibitoci a Zirin Gaza a daidai lokacin da Isra’ila ke ci gaba da kai hari Falasdinu.

Firaiministan Iraki, Mohammed Shia al-Sudani ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.

Asibitoci na fama da tsananin karancin manfetur a Gaza. Hoto/Reuters

Sanarwar ba ta bayyana ranar da za a kai man fetur din ba ko kuma yadda za a shigar da shi cikin Gaza duk da kawanyar da aka yi.

Har yanzu Isra’ila ba ta bari an shiga da man fetur cikin Gaza ba tun bayan soma wannan rikicin.

0800 GMT — Sojin Isra'ila sun kama 'yan jarida biyu a birnin Hebron

Rundunar sojin Isra’ila ta kama ‘yan jarida biyu a Gabar Yamma da Kogin Jordan a ranar Laraba.

Wadanda suka shaida lamarin sun sanar wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa an kama Mohamed al-Atrash da Amer Abu Arafa bayan sojojin na Isra’ila sun kai samame gidajensu da ke birnin Hebron inda suka gudanar da bincike.

Sama da 'yan jarida 36 aka kashe tun bayan soma wannan rikici tsakanin Isra'ila da Falasdinawa. Hoto/Reuters

Rahotanni sun kuma ce sojojin na Isra’ila sun tsare wasu jama’ar a Hebron da Bethlehem da Ramallah da Nablus da Qalqilya da Jericho.

0325 GMT — Saudiyya ta ce za ta karbin bakunci taron Kungiyar Hadin Kan Kasashen Musulmai don tattauna yakin Gaza

Isra'ila na ci gaba da luguden wuta a Gaza. Hoto: Reuters

Ministan zuba jari na Saudiyya ya ce nan da kwanaki masu zuwa kasar za ta karbi bakuncin taron koli na kasashen Larabawa da kasashen Musulmai domin tattaunawa kan yakin Isra'ila da Falasdinu.

"Za mu gani a cikin 'yan kwanaki masu zuwa, Saudiyya ta kira wani taron gaggawa na Larabawa a Riyadh," in ji ministan zuba jari na Saudiyya, Khalid Al-Falih, a taron Bloomberg New Economy Forum a Singapore.

“Nan da ‘yan kwanaki za ku ga kasar Saudiyya na gudanar da taron kasashen Musulmai,” in ji shi.

"A cikin kankanin lokaci, makasudin gabatar da wadannan tarukan guda uku da sauran tarukan karkashin jagorancin Saudiyya shi ne a kai ga warware rikicin cikin lumana."

Kamfanin dillancin labaran Etemad ya rawaito cewa, shugaban kasar Iran Ibrahim Raisi zai tafi Saudiyya a ranar Lahadi mai zuwa don halartar taron kolin Ƙungiyar Hadin kan Ƙasashen Musulmai, wadda ita ce ziyarar farko da wani shugaban kasar Iran ya kai tun bayan Tehran da Riyadh suka kawo karshen rashin jituwar da aka shafe tsawon shekaru ana yi karkashin wata yarjejeniya da China ta kulla a watan Maris.

0300 GMT — An yi tir da kalaman Rashida Tlaib ta yi a kan Isra'ila saboda yaƙin Gaza

Rashida Tlaib ita ce Ba'amurkiya kuma Bafalasɗiniya ɗaya tilo a Majalisar Wakilan Amurka./Hoto: AFP

Majalisar Wakilan Amurka ta kaɗa ƙuri'a don hukunta 'yar Jam'iyyar Democrat dmai wakiltar Michigan, Rashida Tlaib - Ba'amurkiya kuma Bafalasɗiniya ɗaya tilo a Majalisar - tsawatawar mai ban mamaki.

Kuri'un da aka kaɗa 234-188 na zuwa ne bayan isassun 'yan jam'iyyar Democrat sun haɗa kai da 'yan Republican don tsawatarwa Tlaib, a wani hukunci wanda daga irinsa sai kora daga majalisar.

'Yar majalisar da ta shafe wa'adi uku ta daɗe tana shan suka kan ra'ayoyinta kan rikicin da aka kwashe shekaru da dama ana yi a Gabas ta Tsakiya.

Dan majalisar wakilai na Republican Rich McCormick na Georgia ne ya ingiza ɗaukar wannan matakin a matsayin martani ga abin da ya kira kambama kalaman nuna ƙyama da Tlaib ke yi. Ya ce ta "yi ƙarairayi da dama a game da babbar ƙawarmu, Isra'ila, da harin da aka kai ranar 7 ga Oktoba."

Tlaib, wacce wasu 'yan jam'iyyar Democrat ke goyon bayanta, ta kare matsayinta, tana mai cewa "ba zan yi shiru ba kuma ba zan bar ku sauya maganata ba."

Tlaib ta kara da cewa sukar da take yi wa Isra'ila a ko da yaushe tana yi ne a kan gwamnatin ƙasar da kuma jagorancinta a karkashin Firayim Minista Benjamin Netanyahu.

"Yana da mahimmanci a dinga raba batun mutane da na gwamnati," in ji ta. "Ra'ayin cewa sukar gwamnatin Isra'ila abu ne na ƙyamar Yahudawa abu ne mai hatsarin gaske. Kuma an yi amfani da shi wajen rufe bakunan mutane daban-daban na kare hakkin bil'adama a fadin kasarmu."

TRT Afrika da abokan hulda