| Hausa
WASANNI
2 minti karatu
Maroko: An fitar da ƙasar Afirka guda da ta rage daga gasar Kofin Duniya
Kylian Mbappe ya huce haushin fenaretin da ya ɓarar a zagayen farko na wasan, inda ya ci ƙwallo guda cikin biyun da suka bai wa Faransa nasarar ci 2-0 kan Maroko a matakin kwatafainal na gasar Kofin Duniya ranar Alhamis.
Maroko: An fitar da ƙasar Afirka guda da ta rage daga gasar Kofin Duniya
An fitar da Maroko daga gasar cin kofin duniya ta FIFA ta shekarar 2026 a ranar 9 ga watan Yuli, 2026.

A ƙarshe dai, an fitar da duka ƙasashen Afirka 10 daga gasar Kofin Duniya da ke gudana a Amurka, Canada, da Mexico, yayin da ake kammala matakin kwata-fainal na gasar ta FIFA 2026.

Maroko ta zama ƙasar Afirka ta ƙarshe da ta bar gasar, bayan da Faransa ta doke ta da ci 2-0 a wasan da suka buga a maraicen Alhamis.

Wasan ya gudana a gaban ‘yankallo 63,811 a filin wasa na garin Boston, kuma ya yi kama da wasan zagayen semi-fainal na gasar Kofin Duniya na 2022, inda Faransa ta fitar da Maroko.

Kylian Mbappé ne ya ci ƙwallon farko a minti na 60, inda ya huce haushinsa na ɓarar da bugun fenaretin da ya samu tun a minti na 28.

Minti shida bayan nan, Ousmane Dambele ya ci ƙwallo ta biyu kuma aka tashi wasan Faransa na da ci biyu, Maroko babu ci.

Tunkarar Sifaniya ko Belgium

Wannan ce ƙwallo ta takwas da Mbappé ya zura a gasar, lamarin da ya sa ya sake kamo Lionel Messi a yawan ƙwallaye a gasar ta bana, da ƙwallo takwas.

Zuwa yanzu, tauraron tawagar ya zura ƙwallaye 20 a cikin wasanni 20 na gasannin Kofin Duniya, wanda ke nufin da ƙwallo ɗaya kaɗai Messi ya wuce shi a jimillar lissafi.

Nasarar ta Faransa na nufin tawagar za ta kara da Sifaniya ko Belgium a garin Dallas ranar Talata mai zuwa a zagayen dab da na ƙarshe.

Faransa na ƙoƙarin maimaita kaiwa wasan ƙarshe na Kofin Duniya a karo na uku a jere ƙarƙashin koci Didier Deschamps, wanda ya shirya murabus bayan kammala gasar.

Kocin ya kai tawagar ga nasarar lashe kofin a 2018, sai suka zo na biyu a 2022, kuma a yanzu ma ana ganin Faransa za ta samu sauƙin kaiwa ga wasan ƙarshe.