Amurka ta hana shugaban Falasɗinawa Mahmoud Abbas biza don halartar Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya (UNGA) wanda za a yi a makon gobe a birnin New York, a cewar wata majiya da ke da masaniya kan lamarin.
A ranar Laraba ne Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ce ta miƙa rahoto ga Majalisar Dokokin ƙasar kan cewa, Kungiyar 'Yantar da Falasɗinawa (PLO) da Hukumar Falasɗinawa (PA) sun sake gaza cika alƙawuran da suka ɗauka a ƙarƙashin dokokin Amurka, tana mai nuni kan matakan da aka ɗauka a ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa, ciki har da "sanya rikicin Isra'ila da Falasɗinawa ya zama na duniya a Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya (ICC) da Kotun Shari'a ta Duniya (ICJ)."
Ta kuma ambaci ƙoƙarin jami'an Falasɗinawa na "kauce wa tattaunawa ta hanyar yarda da matsayar wata Ƙasa ko fiye da suka amince da Falasɗinu a matsayin ƙasa, ba tare da an jira a cim ma yarjejeniyar ƙarshe ba.
Ma'aikatar ta kuma zargi PLO da PA da "ci gaba da biyan alawus ga 'yanta'adda da kuma ɗaukaka ayyukan ta'addanci a cikin sanarwarsu ga jama'a da littattafan karatu na makaranta."
"Sakamakon gazawarsu wajen yin garambawul ... Amurka za ta tsawaita takunkuminta na hana mambobin PLO da jami'an PA izinin shiga ƙasarta," in ji ma'aikatar a cikin wata sanarwa.
Mataki na biyu
Matakan na zuwa ne gabanin babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81, wanda za a fara a mako mai zuwa a birnin New York.
Kazalika sanarwar ta biyo bayan irin wannan mataki da Amurka ta ɗauka a bara, lokacin da Washington ta hana ko ta soke bizar jami'an PLO da PA kafin babban taron na MDD a 2025, duk da kiraye-kirayen da ƙawayen Amurka suka yi na a sake duba lamarin.
Ofishin Jakadancin Hukumar Falasɗinu a MDD ya samu sassauci a ƙarƙashin Yarjejeniyar Hedikwatar Majalisar Ɗinkin Duniya, kana daga baya ofishin Shugaba Mahmoud Abbas ya buƙaci Amurka da ta janye matakin.
Abbas bai samu damar halartar Babban Taron na bara da kansa ba, sai dai ya yi jawabi ta hanyar intanet.
Rahotanni a ranar Laraba sun ce Amurka ta sake maimaita matakin da ta ɗauka a bara na kin amincewa da neman bizar Abbas zuwa taron UNGA na wannan shekarar, tare da na sauran jami'an Falasɗinu.



















