Kunkuru Jonathan: Dabba mafi tsufa da ya kwashe shekaru 193 a duniya
Gwamnatin tsibirin Saint Helena ta ayyana ranar 4 ga Disamba,1832 a matsayin ranar haihuwar Jonathan a hukumance / Others
Kunkuru Jonathan: Dabba mafi tsufa da ya kwashe shekaru 193 a duniya
An yi imanin cewa an haifi kunkurun mai suna Jonathan ne a shekarar 1832 a Seychelles, wurin zuwa yawon bude ido mai yawan jama'a a Afirka.
23 Janairu 2026

Jonathan, dabba mai jan ciki mafi tsufa a duniya, har yanzu yana cikin koshin lafiya duk kuwa da tsufansa kuma yana taimaka wa masana kimiyya ilimin ƙara sani game da tsawon lokacin da kunkuru zai iya rayuwa.

An haife shi a shekarar 1832 a Seychelles, wata ƙasa da ake yawan zuwa yawon buɗe ido a Afirka.

Ya yi bikin cika shekaru 193 a ranar 4 ga Disamban 2025. Wannan ba wai kawai ranar haihuwa ba ce— hakan na tabbatar da matsayinsa na dabbar ƙasa mafi tsufa da aka taɓa samu, matsayin da kambun tarihin Duniya wato ‘Guinness World Record’ ya amince da shi a hukumance.

A yanzu haka Jonathan na zaune a wani yanki na Birtaniya na Saint Helena, wanda tsibiri ne da ke Kudancin Tekun Atlantika, a gabar tekun kudu maso gabashin ƙasashen Angola da Namibia wadanda ke zama mafi kusa da yanki.

Labarin rayuwarsa mai ban mamaki a tsibirin mai nisa ya fara ne a shekarar 1882, lokacin da 'yan mulkin mallaka na Birtaniya suka kawo shi tare da wasu dabbobi masu jan ciki da dama yana da shekaru kusan 50.

Tun daga lokacin yake zaune a filin Gidan Gona na gwamnan mulkin mallaka, inda ya zama wurin yawon bude ido.

Tsawon rayuwar da Jonathan ya yi, na da matukar ban mamaki, wanda ya shafi mulkin sarakuna takwas na Birtaniya, ciki har da Sarauniya Elizabeth ta Biyu, da shugabannin Amurka 40.

Duk da cewa an kiyasta shekarun Jonathan, a watan Nuwamba na 2022 ne gwamnatin Tsibirin Saint Helena ta ayyana ranar 4 ga Disamba, 1832 a matsayin ranar haihuwar Jonathan a hukumance.

Kunkuru na daga cikin dabbobin da suka fi tsawon rai a duniya, inda manyan kunkuru na Seychelles ke da matsakaicin tsawon rai na shekaru 150, kuma daga shekaru 50 ake fara daukarsu a matsayin waɗanda suka girma.

Duk da rasa ganinsa da kuma daina shaƙar wari da ƙamshi saboda tsufansa, ruhin Jonathan bai yi rauni ba.

A ƙarkashin kulawar likitocin dabbobi, yana samun abinci mai kyau da gina jiki na 'ya'yan itatuwa da kayan lambu da ake ciyar da shi da su.

Jonathan, wanda ya yi fice kuma ake sonsa, an manna hotonsa a kan kudin Saint Helena da kuma tambarin yankin.

A kowace shekara, jami'ai sukan yi masa bikin zagayowar ranar haihuwarsa tare da yanka kek wanda ya dace dabbar.

A yanayin sauyi akai-akai a duniya, Jonathan ya zama abin tarihi mai rai - wata dabba mai sauƙi da tafiya a hankali da nuna juriya, wanda ke ci gaba da nuna yanayi na jin daɗi, kiwo, da kuma lokaci da ke wucewa a hankali har zuwa yanzu.