| hausa
TURKIYYA
3 MINTI KARATU
Erdogan ya jaddada cewa Turkiyya na tare da Somalia a yakin da take da ta’addanci
Shugaba Erdogan ya bayyana cewa ya kamata a daina tashin hankalin da ake yi tsakanin Somalia da Ethiopia a wani yanayi na mutunta iyakokin kasar Somalia a wata tattaunawar da ya yi da takwaransa na Somalia.
Erdogan ya jaddada cewa Turkiyya na tare da Somalia a yakin da take da ta’addanci
Shugabannin sun yi musayar ra'ayi kan wasu batutuwa suna masu jaddada muhimmancin hadin kai tsakanin Turkiyya da Somalia wajen tunkarar kalubalen da suke da su tare da ba da gudunmawa wajen tabbatar tsaro a yankin. /Hoto: AA
5 Janairu 2024

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya zanta ta waya da Shugaba Hassan Sheikh Mohamoud na Somalia, inda suka tattauna kan dangantaka tsakanin Turkiyya da Somalia, da kokarin yaki da ta’addanci da kuma lamuran duniya da na yankin.

A lokacin zantawar da suka yi ranar Juma’a, Shugaba Erdogan ya bayyana cewa Turkiyya tana tare da Somalia a yakin da take yi da ta’addanci kuma hadin kai tsakanin kasashen biyu zai ci gaba da inganta.

An yi tattaunawar ne kan dangantaka tsakanin Turkiyya da Somalia, da yaki da ta’addanci da kuma batutuwan duniya da na yankin.

Shugaba Erdogan ya bayyana fatansa na ganin an kawo karshen tashin hankali tsakanin Somalia da Ethiopia a wani yanayi na mutunta iyakar kasar Somalia.

Shugabannin biyu sun yi musayar ra'ayi kan batutuwa daban-daban, suna masu jaddada muhimmancin hadin kai tsakanin Turkiyya da Somalia wajen tunkarar kalubalen da ke gabansu tare da ba da gudunmawa wajen tabbatar da zaman lafiyar yankin.

Turkiyya ta damu game da yarjejeniyar da Ethiopia da Somaliland suka kulla

Ranar Alhamis Turkiyya ta fitar da sanarwar goyon baya da kare martabar iyakokin Somalia bayan wata yarjejeniya da Ethiopia da Somaliland suka kulla wadda za ta bai wa Ethiopia damar amfani da tashar jiragen ruwan Somaliland da ke Tekun Maliya.

"Yarjejeniyar Fahimtar Juna don Hadin Kai da Aiki Tare da aka sanya hannu a kai a Addis Ababa a ranar 1 ga Janairu, 2024 tsakanin Jamhuriyar Ethiopia da Somaliland, ba tare da sani da yardar gwamnatin Somalia ba, na sanya damuwa," in ji Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya a wata sanarwa da ta fitar.

Firaministan Ethiopia Abiy Ahmed da Shugaban Kasar Somaliland Muse Bihi Abdi ne suka sanya hannu kan yarjejeniyar a ranar Litinin.

Ethiopia da ba ta da iyaka da teku ta sanya hannu da yankin Somaliland da ya balle daga Somalia, don amfani da Tashar Jiragen Ruwa ta Berbera.

MAJIYA:TRT Afrika
Rumbun Labarai
Turkiyya na jimamin tunawa da rasuwar Ataturk shekara 87 da suka wuce
Nasarar da aka samu a yankin Karabakh na Azerbaijan babbar nasara ce ga yankin Caucasus: Erdogan
Turkiyya ta yi umarnin kama Firaministan Isra'ila Netanyahu da wasu mutane kan kisan kiyashi a Gaza
Turkish Airlines ya sayi hannun jari na dala miliyan 355 a kamfanin Air Europa na Spain
Erdogan ya yi Allah wadai da kashe fararen-hula a birnin Al Fasher na Sudan
Za a gudanar da tattaunawa a Istanbul kan yarjejeniyar tsagaita wutar Gaza da matsalolin jinƙai
Tsarin duniya na yanzu ya fi ba da fifiko kan iko fiye da adalci: Babban Daraktan TRT Sobaci
Hamas ba ta da nukiliya, amma Isra'ila na da su: Erdogan ya nemi Berlin ta ɗauki mataki kan Tel Aviv
Ana shirin fara taron TRT World Forum karo na 9 a Istanbul
Cikin hotuna: Yadda aka yi bukukuwa a duk faɗin kasa na cikar Ranar Jamhuriya ta Turkiyya ta 102
Turkiyya ta yi kira a tsagaita wuta nan-take a yaƙin da ake yi a birnin Al Fasher, Sudan
Turkiyya za ta mika wa dakarunta tankar yaki ta Altay da aka samar da yawa a karon farko
Kungiyar ta'addanci ta PKK ta sanar da janyewa baki ɗaya daga Turkiyya
Babu wani lissafin siyasa ko na tsaro da zai yiwu a duniya ba tare da Turkiyya ba: Erdogan
Rumfar Karfe: Fasahar Turkiyya ta cikin gida mai aiki da Ƙirƙirarriyar Basira a sabon zamanin tsaro
Shugaba Erdogan ya shirya ziyartar yankin Gulf don haɓaka alaƙar tattalin arziki da ƙawance
Turkiyya ta yi maraba da yarjejeniyar tsagaita wutar Afghanistan da Pakistan
An Fara Taron Yaki da Shara na ‘Zero Waste’ a Istanbul karkashin jagorancin Emine Erdogan
Matar Shugaban Turkiyya Emine Erdogan ta yi kira a bunkasa shigar mata cikin harkokin duniya
Cinikayya tsakanin Turkiyya da Afirka ta wuce $37b ana sa ran ta kai $40b a 2025: Minista