| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
Ebola ta shafi kusan makarantu 100 a gabashin Jamhuriyyar Dimokuradiyyar Kongo
A lardin Ituri, makarantu 55 sun bayar da rahoton samun ɗalibai 64 da aka tabbatar sun kamu da cutar, ciki har da mutum 33 da suka mutu, a cewar hukumomin lardin.
Ebola ta shafi kusan makarantu 100 a gabashin Jamhuriyyar Dimokuradiyyar Kongo
Daga cikin ɗalibai 64 da aka tabbatar sun kamu da cutar a Ituri, mutum 24 sun warke, yayin da wasu bakwai ke ci gaba da samun kulawa / Reuters (Wire)
 

Kusan makarantu 100 a gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo sun bayar da rahotannin bullar cutar Ebola tun bayan fara sabuwar shekarar karatu a watan Satumba, inda cutar ta yi sanadin mutuwar ɗalibai da dama, a cewar bayanan hukuma da aka fitar ranar Juma’a.

A lardin Ituri, makarantu 55 sun bayar da rahoton samun ɗalibai 64 da aka tabbatar sun kamu da cutar, ciki har da mutum 33 da suka mutu, a cewar hukumomin lardin.

Haka kuma, makarantu 44 a maƙwabciyarta, lardin Kivu ta Arewa, sun fuskanci matsalar, inda kusan ɗalibai 50 suka kamu da cutar, yayin da 31 daga cikinsu suka mutu.

Daga cikin ɗalibai 64 da aka tabbatar sun kamu da cutar a Ituri, mutum 24 sun warke, yayin da wasu bakwai ke ci gaba da samun kulawa a cibiyoyin kula da masu fama da cutar.

An sake buɗe makarantu a gabashin Kongo a farkon watan Satumba domin fara sabuwar shekarar karatu, duk da damuwar da ake nunawa kan barkewar cutar Ebola.

Ministar Ilimi, Raissa Malu, ta yi kira ga cibiyoyin ilimi da su “ƙarfafa matakan kariya daga cutar”.

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce, bayan shafe watanni shida ana fama da annobar, cutar na ci gaba da yaɗuwa zuwa wasu yankuna, musamman wuraren da rikice-rikicen makamai suka shafa. Ana samun sabbin waɗanda suka kamu da cutar tsakanin 400 zuwa 500 a kowane mako.

Bayanai na baya-bayan nan da Cibiyar Turai ta Kula da Cututtuka da Rigakafinsu ta fitar sun nuna cewa an samu fiye da mutum 11,500 da aka tabbatar sun kamu da cutar, yayin da mutum 5,600 suka mutu tun bayan barkewar annobar a watan Mayu.

Hukumomin lafiya sun bayyana rashin tsaro a matsayin babban ƙalubale wajen shawo kan annobar.

A ranar Laraba, Darakta-Janar na WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce har yanzu annobar na matsayin babbar barazana ta ƙasa da ƙasa ga lafiyar.