| Hausa
TURKIYYA
3 MINTI KARATU
Shugaban Falasɗinawa Mahmoud Abbas ya yi jawabi a Majalisar Dokokin Turkiyya
Abbas ya ce Falasdinawa na matukar yabawa da kakkausan matakin da Turkiyya ta dauka na ƙin amincewa da kuma yin Allah wadai da "yakin kisan kare dangi da Isra'ila ke yi kan Falasdinawa."
Shugaban Falasɗinawa Mahmoud Abbas ya yi jawabi a Majalisar Dokokin Turkiyya
Shugaban Falasdinawa Abbas na jawabi ga majalisar dokokin Turkiyya a Ankara/ Hoto: Reuters / Reuters

A ziyarar da ya kai Turkiyya a wani muhimmin lokaci, shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas ya yi jawabi a gaban majalisar dokokin Turkiyya a wani zama na musamman da aka yi, wanda aka kira domin nuna goyon baya ga fafutukar Falasdinu.

Da yake ƙarin haske kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa yankunan Falasdinawa, musamman Gaza, Abbas a ranar Alhamis ya jaddada cewa "Falasdinawa sun tsaya ƙyam wajen adawa da masu tsananin kishin kafa ƙasar Falasɗinu da ke neman mamaye yankin baki daya."

Abbas ya kuma ce Falasdinu ta yi matuƙar godiya ga kakkausan matakin da Turkiyya ta ɗauka na ƙin amincewa da yin Allah wadai da "yaƙin kisan ƙare dangi da Isra'ila ke yi kan Falasdinawa."

Ya kara da cewa, "Muna kira ga dukkan jama'a da su tsaya tare da mu wajen 'yantar da fursunonin Falasdinawan sama da 10,000 da ke tsare a gidajen yarin Isra'ila," yana mai kira ga ƙasashen duniya da su dauki matakin gaggawa da inganci wajen tsagaita wuta ta dindindin.

Abbas ya ci gaba da jaddada cewa, "Gaza da Gabashin Kudus, da Yammacin Gabar Kogin Jordan, yanki ne guda daya da ya kafa kasar Falasdinu mai cin gashin kanta bisa dokokin kasa da kasa."

Zargin kisan ƙare dangi

Isra'ila ta fuskanci Allah wadai daga ƙasashen duniya saboda yin watsi da ƙudirin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya wanda ya buƙaci a tsagaita wuta cikin gaggawa.

Sojojin Isra'ila sun kashe Falasdinawa sama da 40,000 a Gaza, yawancinsu mata da kananan yara, a cewar hukumomin lafiya na Falasdinu.

Fiye da watanni goma a cikin yakin Isra'ila, yankunan Gaza da yawa sun zama kufai kuma sun kasance a cikin ƙawanyar hana shigar musu da abinci da ruwa mai tsabta, da magunguna.

Ana zargin Isra'ila da kisan kiyashi a kotun kasa da kasa, wacce a hukuncinta na baya-bayan nan ta umarci Tel Aviv da ta gaggauta dakatar da kai hare-hare a kudancin birnin Rafah, inda Falasdinawa sama da miliyan daya suka nemi mafaka.

MAJIYA:TRT World
Rumbun Labarai
Haɗin gwiwar Turkiyya da Afirka na da burin faɗaɗa damar tattalin arziki ga mata
Shugaban Turkiyya Erdogan da Firaministan Libya sun tattauna a Ankara
Turkiyya ta rattaba hannu kan yarjejeniyoyin da ƙimarsu ta kai $5.1B a taron COP31
Erdogan na so manyan ƙasashe su yi ƙaimi a yaƙi da sauyin yanayi, ya yi Allah wadai da lalata Gaza
Erdogan ya gudanar da jerin ganawa da shugabannin ƙasashe daban-daban a taron COP31
Taron COP31 a Turkiyya ya mayar da hankali kan tsaron makamashi da sufuri mai tsafta
Kurum ya buƙaci taron COP31 ya mayar da alƙawuran yaƙi da sauyin yanayi zuwa ayyuka na zahiri
Erdogan da shugaban Nijar sun tattauna batun tsaro da dangantakar kasashen biyu ta wayar tarho
COP31: Shugabannin duniya za su dasa itatuwan zaitun a bikin ranar dashen itatuwa ta ƙasa a Turkiyya
Za a fara taron COP31 a Turkiyya yayin da ake kiran ɗaukar matakai masu ƙarfi kan sauyin yanayi
Duran na Turkiyya ya yi gargaɗi game da babakere kan algorizin a duniyar dijital
Turkiyya na shirin karɓar baƙuncin babban taron COP31 kan sauyin yanayi a Antalya
Erdogan ya ce ‘Dole a yi aiki da yarjejeniya’ a Gaza, ya soki ta’addancin kama wuri zaunan Isra'ila
Turkiyya za ta zuba jarin dala miliyan 400 a shirin sararin sama, za ta samar da cibiya a Somalia
Matar Shugaban Turkiyya, Emine Erdogan, ta buɗe cibiyar al'adu ta Yunus Emre a Koriya ta Kudu
Turkiyya da Koriya ta Kudu sun sa hannu kan yarjejeniyar gina tashar makamashin nukiliya
Erdogan na nema cinikayyar dala biliyan 15 da ƙarin muhimmiyar dangantaka a ziyararsa Koriya ta Kudu
Erdogan na Turkiyya: 'Babu wata damar rarrabuwar kai a duniyar Turkawa'
'Turkiyyar yau ta fi ta bara karfi,' in ji Shugaba Erdogan a Ranar Jamhuriya
Turkiyya ta yi bikin cika shekaru 103 da kafa Jamhuriyarta