TURKIYYA
2 minti karatu
Matar Shugaban Turkiyya ta yi kira kan samar da tsari ilimi mai daraja a duniya a taron Kiev
Emine Erdogan ta jaddada cewa ilimi shi ne babban makamin magance matsalolin duniya, tana mai bayani kan shirye-shiryen Turkiyya na ayyukan taimako da jinƙai.
Matar Shugaban Turkiyya ta yi kira kan samar da tsari ilimi mai daraja a duniya a taron Kiev
Ta jaddada ƙuduri na ƙasar Turkiyya game da ƙa'idojin ɗan'adam a fannin ilimi. / Hoto: Reuters
12 Satumba 2025

Matar Shugaban Kasar Turkiyya, Emine Erdogan ta halarci Taron Koli na Biyar na Matan Shugabannin Ƙasashe da Mazajensu, wanda Matar Shugaban Kasar Ukraine, Olena Zelenska ta shirya a birnin Kiev, inda ta yi jawabi ta bidiyo.

Taron, wanda aka gudanar karkashin taken “Ilimi Mai Gina Duniya,” ya tara matan shugabanni da ƙwararrun ƙasa da ƙasa da masu tsara manufofi don tattauna yadda ilimi zai iya ƙarfafa juriya, zaman lafiya da ci-gaban al’umma.

Haka kuma, an gabatar da wani bincike na kasa da kasa mai taken “Ilimi a Matsayin Makamin Gina Juriya, Babban Jarin Al’umma, da Al’adar Zaman Lafiya,” wanda aka gudanar a kasashe 14—ciki har da Turkiyya—tare da shigar da ra’ayoyin dalibai da malamai da iyaye.

Matar Erdogan ta bayyana ilimi a matsayin mafi karfin kayan aiki wajen fuskantar kalubalen yau.

A duniyar da ke fama da jarrabawar rayuwa kamar yunwa da talauci da yaki da ƙaura da kuma sauyin yanayi, abu ɗaya da zai iya taimaka wa bil'adama sake farfaɗowa, tabbas shi ne ilimi,” in ji ta a cikin wata sanarwa a ranar Juma’a.

Ta ƙara da cewa “tsarin ilimi mai dogaro da dabi’u da dabi’un kirki” da kuma samun damar ilimi ga kowa da kowa zai iya samar da duniya mai adalci da daidaito.

Ta kuma jaddada sadaukarwar Turkiyya ga ka’idojin jinƙai a fannin ilimi, tana nuna cibiyar Türkiye Maarif Foundation, wacce ke aiki a kasashe 55, a matsayin wata babbar cibiyar da ke bayar da ilimi mai ƙunshe da zaman lafiya.

“Manufarmu ita ce tabbatar da cewa yara masu karancin dama za su iya amfani da hakkinsu na samun ilimi kuma su samu matsayi a duniya ta nan gaba cikin daidaito,” in ji ta.

Ta kammala da godiya ga wadanda suka shirya shirin tare da bayyana fatanta na “makoma inda rikice-rikicen jinƙai za su kawo karshe kuma za mu hadu a gobe mai albarka.”

“Ina fatan wannan taro mai ma’ana, wanda ke bayar da gudunmawa ga makomar bil’adama, zai zama hanyar fara sabbin abubuwa.”