Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya soma wata ziyara a Qatar a ranar Litinin, inda zai halarci taron gaggawa na Ƙasashen Larabawa da Musulmai da za a gudanar bayan harin da Isra'ila ta kai a Doha a makon jiya.
Shugaba Erdogan ya samu rakiyar matarsa Emine Erdogan, da shugaban hukumar leƙen asiri ta ƙasa (MIT) Ibrahim Kalin, da Akif Cagatay Kilic, da kuma babban mai bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Ƙasashen Waje da Tsaro, Daraktan Dadarwa Burhanettin Duran, da Mataimakin Shugaban Jam'iyyar Justice and Development (AK) Halit Yerebakan.
Taron Ƙasashen Larabawa da Musulmai a birnin Doha ya hada shugabannin ƙasashe da manyan jami'ai da dama daga sassan yankin.
Qatar ce ta kira taron a matsayin martani ga harin da Isra'ila ta kai kan shugabannin Hamas a Doha a makon jiya, inda aka kashe mambobin kungiyar biyar da jami'in tsaron Qatar guda ɗaya.
"Lokaci ya yi da ƙasashen duniya za su daina fuska biyu kana su hukunta Isra'ila kan dukkan laifukan da ta aikata," in ji Firaministan Qatar kuma Ministan Harkokin Wajen Ƙasar, Sheikh Mohammed bin Abdulrahman Al Thani a wani taro da aka gudanar a ranar Lahadi.
"Wannan gwamnatin ta kai hare-hare kan Ƙasashen Musulmai da dama waɗanda suka hada da Qatar, da Lebanon, da Iraƙi, da Iran da kuma Yemen," in ji shi.
Ya ƙara da cewa "Tana yin duk abin da ta ga dama, kuma abin takaici ne, Amurka da Ƙasashen Turai ma suna goyon bayan wadannan munanan ayyukan."
Qatar tare da Amurka da Masar, sun kasance masu shiga tsakani a tattaunawar kawo ƙarshen yakin da Isra'ila ke yi a Gaza, inda aka kashe kusan Falasdinawa 65,000 tun daga watan Oktoban 2023.