TURKIYYA
2 minti karatu
Shugaban Turkiyya Erdogan ya karbi sabon samfurin motar Togg T10F da aka ƙera a ƙasar
Shugabannin Togg sun miƙa motar lantarkin ga shugaban inda ya yi gwajin tuki da motar mai launin shuɗi, wadda aka liƙa mata tambarin shugaban ƙasa a wurin lambar motar.
Shugaban Turkiyya Erdogan ya karbi sabon samfurin motar Togg T10F da aka ƙera a ƙasar
Togg ya sanar da cewa za a fara karɓar odar T10F a Turkiyya daga ranar 15 ga Satumba, sannan a Jamus daga ranar 29 ga Satumba. / AA
13 Satumba 2025

Kamfanin ƙera motocin lantarki na Turkiyya, Togg, ya gabatar da sabon samfurinsa na T10F fastback ga Shugaba Recep Tayyip Erdogan, inda aka ba shi damar duba ƙirar motar da fasalinta da sabbin fasahohin da aka haɗa a cikin motar yayin bikin miƙa ta.

Shugabannin Togg sun miƙa motar lantarkin ga shugaban inda ya yi gwajin tuki da motar mai launin shuɗi, wadda aka liƙa mata tambarin shugaban ƙasa a wurin lambar motar.

A lokacin da ake jawabi yayin miƙa motar, an sanar da Erdogan game da fasalin motar da kuma yadda motar ke aiki kafin a miƙa masa ita a hukumance.

Bayan gwajin tukin, Ministan Masana'antu da Fasaha Mehmet Fatih Kacir da Shugaban Togg, Fuat Tosyali, sun miƙa wa Erdogan kyautar tunawa da wannan rana.

Shugaban Sadarwa na Turkiyya, Burhanettin Duran, ya halarci bikin miƙa motar na farko, inda ya jaddada goyon bayan gwamnati ga masana'antar ƙera motoci ta cikin gida.

Taurari biyar a gwajin Euro NCAP

Togg ya sanar da cewa za a fara karɓar odar T10F a Turkiyya daga ranar 15 ga Satumba, sannan a Jamus daga ranar 29 ga Satumba.

Gabatarwar ta yi daidai da fitowar Togg a kasuwar Turai ta IAA Mobility 2025 da aka gudanar a Munich, wani babban biki na masu ƙera motoci, kamfanonin fasaha, da masu kirkirar hanyoyin sufuri.

Kamfanin ya nuna jerin motocinsa na lantarki da tsarin sufuri ga 'yan jarida na cikin gida da na ƙasashen waje a ranar da aka ware domin manema labarai a taron.

Togg ya jaddada burinsa na zama "fiye da mota kawai" tare da nuna sabbin fasahohi da gasa a duniya a fannin kera motoci.

Dukkanin samfurorin T10X da T10F sun samu mafi girman taurari biyar a duka gwaje-gwajen tsaro na Euro NCAP, suna cika ka'idojin kasuwar Turai.

Kaddamarwar ta ƙarfafa dabarun Togg na faɗaɗa kasuwancinta a duniya tare da sanya Turkiyya a matsayin mai tasowa a fannin fasahar kera motoci masu ɗorewa da ci gaba.