TURKIYYA
2 minti karatu
A shirye Turkiyya take ta taimaka wa ƙasashe ‘yan’uwanta da ƙarfin tsaro: Erdogan
Shugaban Turkiyya ya jaddada ‘‘goyon bayan ƙasarsa’’ ga Qatar, yana mai Allah wadai da harin da Isra'ila ta kai kan tawagar Hamas a Doha kana ya bayyana hakan da ‘‘ta’addanci da ya kai wani mataki na daban’’.
A shirye Turkiyya take ta taimaka wa ƙasashe ‘yan’uwanta da ƙarfin tsaro: Erdogan
Al'ummar Musulmai suna da "hanyoyi da damar dakile manufar faɗaɗa yakin Gabas ta tsakiya na Isra'ila," in ji Shugaba Erdogan / AA
9 awanni baya

Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi kira ga al'ummar Musulmai a faɗin duniya da su ƙara matsa lamba kan Isra'ila, yana mai cewa dole ne a yi amfani da matakan tattalin arziki wajen rage ƙarfin Tel Aviv.

"Dole ne mu ƙara kaimi a fannin diflomasiyya don ƙara ƙaƙaba wa Isra'ila takunkumi," in ji Erdogan, yana mai gargaɗin cewa manufar gwamnatin Netanyahu ita ce "ci gaba da kisan kiyashi da ƙare-dangi a Falasɗinu tare da haifar da rashin kwanciyar hankali a yankin".

Da yake jawabi a wajen taron ƙasashen Larabawa da Musulmai da aka gudanar a birnin Doha a ranar Litinin, shugaban na Turkiyya ya jaddada cewa ƙasashen Musulmai suna da ‘dama da kuma ƙarfin hana Isra’ila cim ma manufarta ta faɗaɗa ikonta a yankin’’, yayin da ya yi tir da abin da ya bayyana a matsayin ‘tsarin ta’addancin Isra’ila na tayar da hankali da zubar da jini’’.

"A shirye Turkiyya take don haɗa ƙarfin tsaro da ƙasashe da ke da 'yan uwantaka," in ji shugaba Erdogan.

"Dole ne mu ƙarfafa haɗin gwiwarmu don samun nasara a shekaru masu zuwa."

Kazalika, ya jaddada goyon bayan Turkiyya ga Qatar, inda ya yi Allah wadai da harin da Isra'ila ta kai kan tawagar Hamas a Doha yana mai kwatanta hakan da ta’addanci da ya kai wani mataki na daban’’