Gwamnatin Trump ta gasgata cewa jami’an sojin Amurka sun yi ƙoƙarin kashe kansu sau takwas a lokacin da aka tsawaita aikin wani jirgin ruwan yaƙin Amurka a Gabas ta Tsakiya, kamar yadda wani ɗan majalisar dokokin Amurka ya bayyana a ranar Laraba.
Bayanin ya fito ne a cikin wata wasiƙa da Mukaddashin Sakataren Rundunar Sojin Ruwa ta Amurka, Hung Cao, ya aika a matsayin amsa ga tambayoyin Sanata Kirsten Gillibrand na jam’iyyar Democrat kan halin da ake ciki a cikin jirgin ruwan USS Abraham Lincoln.
Rahotannin taɓarɓarewar yanayin rayuwa da matsalolin lafiyar ƙwaƙwalwa a cikin jirgin tun lokacin da ya fara aiki a teku a watan Nuwamban bara sun ɗauki hankalin kafafen yaɗa labarai a Amurka, lamarin da ya jawo suka kan yaƙin da Amurka ke yi da Iran.
Wasiƙar sakataren sojin ruwan, wanda shi ne babban jami’in farar-hula na rundunar, ta ce: “Tun lokacin da Lincoln ya fara aikin, an samu jumullar ƙoƙarin kashe kai guda takwas a tsakanin rundunar yaƙin.”
Wasiƙar ta ƙara da cewa: “Ba a samu wani mutum da ya kashe kansa a cikin jirgin ba a lokacin wannan aikin.”
Gargaɗi
Wasiƙar ta bayar da ƙarin bayani kan waɗannan ƙoƙarin kashe kai, inda ta ce wani sojan ruwa da aka tura wani ɓangare na rundunar jiragen sama, “ya faɗa cikin teku daga cikin jirgin a farkon watan Agusta”, amma wani jirgin helikwafta mai aikin ceto da neman waɗanda suka ɓace ya gano shi cikin gaggawa, sannan aka fitar da shi daga jirgin domin ci gaba da ba shi kulawar lafiya.
Wani sojan ruwa kuma “ya yi ƙoƙarin tsalle cikin teku a watan Maris, amma abokan aikinsa suka hana shi”, sannan aka mayar da shi zuwa tashar jirgin ruwa ta gida.
Jirgin Lincoln ya bar California a watan Nuwamban 2025 domin gudanar da aiki a Tekun Kudancin China, amma daga bisani aka karkatar da shi zuwa Gabas ta Tsakiya kafin hare-haren Amurka da Isra’ila kan Iran da suka fara a ƙarshen watan Fabrairun 2026. A ƙarshe, ya tsaya a Thailand a farkon watan Satumba, bayan shafe kwanaki 286 a cikin teku.
A watan Agusta, iyalan sojoji da ’yan majalisar dokoki sun yi gargaɗi kan rahotannin ƙoƙarin kashe kai da wasu manyan matsalolin lafiyar ƙwaƙwalwa, ƙarancin abinci da rashin tsafta a cikin jirgin.
Trump ya yi watsi da waɗannan zarge-zargen a lokacin. Shi ma Sakataren Tsaron Amurka, Pete Hegseth, ya dage cewa “ba a bayar da labarin halin da jirgin yake daidai ba.”
















