| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
Sierra Leone ta amince ta karɓi kashin farko na waɗanda aka taso ƙeyarsu daga Amurka
Saliyo ita ce ƙasar Afirka ta baya bayan nan da ta cim ma irin wannan yarjejeniyar da Washington kuma za ta karɓi dala biliyan $1.5 ta tallafa wa shirin
Sierra Leone ta amince ta karɓi kashin farko na waɗanda aka taso ƙeyarsu daga Amurka
TSOHON HOTO: Gwamnatin Shugaba Donald Trump tana ƙoƙarin daƙile shiga Amurka. / Reuters

A ranar Laraba ƙasar Saliyo za ta karɓi kashin farko na ‘yan ci-ranin da aka taso ƙeyarsau daga Amurka, yayin da gwamnatin Shugaba Donald ke ƙara matsa lamba wajen tusa ƙeyar waɗanda take kora zuwa wasu ƙasashe daban maimakon ƙasashen da suka fito.

Ministan harkokin wajen ƙasar Saliyo ya ce jirgi na farko ɗauke da ‘yanci-rani 25 zai isa Freetown babban birnin ƙasar da safiyar Laraba, a ƙarƙashin wata yarjejeniya inda a kowace shekara ƙasar za ta karɓi mutum 300 waɗanda asali ‘yan yammacin Afirka ne.

Saliyo ta shiga jerin ƙasashen Afirka waɗanda suka cim ma irin wannan yarjejeniyar da Washington: Kamaru da Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo da Eswatini da Equatorial Guinea da Ghana da Rwanda da kuma Sudan ta Kudu.

"Muna karɓar waɗanda aka taso ƙeyarsu ne saboda ‘yan asalin yammacin Afirka ne kuma wasu na da takardun Saliyo da suka samu shekaru da dama da suka gabata," kamar yadda Ministan Harkokin Wajen Ƙasar Timothy Musa Kabba ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP ranar Talata.

Zaman kwanaki casa’in

"Suna da ‘yancin zama a ƙasar na kwanaki 90 kuma za su iya komawa gida a ƙasarsu ta asali."

Amurka za ta ba da dala biliyan $1.5 "domin tallafawa da kuɗi na jinƙai da aiki da ke da alaƙa da tsarin", in ji ma’aikatarsa.

Amincewar ƙasashen Afirka ta karɓar ‘yan ci-rani daga Amurka yana zuwa ne tare da tallafin kuɗi na Amurka.

Wasu ƙasashen, irin su Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo, sun yarda su karɓi waɗanda aka taso ƙeyarsu da suka fito daga yankuna na daban, irin su ƙasashen yankin Latin na nahiyar Amurka.