Hukumar Tara Kuɗaɗen Shiga ta Nijeriya (NRS) ta bai wa kamfanonin kirifto da na sauran na hada-hadar kuɗaɗen intanet wa’adin zuwa ranar 30 ga Nuwamban 2026, domin yin rajista a sabon shafinta na haraji, tana mai gargaɗin cewa waɗanda suka ƙi yin hakan za su fuskanci hukunci.
Umarnin ya shafi kamfanonin musayar kuɗaɗen intanet, tura kuɗi, adanawa, cinikayya, biyan kuɗi, bayar da rance da sauran ayyukan kuɗi da suka shafi dijital a Nijeriya.
A sanarwar da ta fitar, hukumar ta ce dole ne kamfanonin su kammala rajista kafin ranar 30 ga Nuwamba, sannan su kammala haɗa tsarin ayyukansu da sabon shafin rajistar haraji kafin ranar 31 ga Disamban 2026.
NRS ta ce matakin ya yi daidai da tanade-tanaden dokokin haraji na shekarar 2025, waɗanda suka wajabta wa masu gudanar da irin waɗannan ayyuka yin rajista, adana bayanan hada-hadarsu, gabatar da rahotanni da biyan haraji.
Hukumar ta kuma bayyana cewa sabon tsarin zai taimaka wajen sa ido kan harkokin kuɗi da kuma yaƙi da safarar kuɗaɗen haram, tallafa wa ta’addanci da yaɗuwar makamai ba bias ƙa’ida ba.
Ta jaddada cewa wajabcin rajistar ya shafi dukkan kamfanonin da ke gudanar da ayyukan kadarorin dijital a Nijeriya ko kuma waɗanda ‘yan ƙasar ke amfani da su, ko da kuwa suna da ofis a cikin ƙasar ko ba su da shi.















