Yadda Christina Koch ta daga tutar Ghana a yayin tafiyarta zuwa Duniyar Wata
Christina Koch daliba ce ta musayar ilimi a Jami'ar Ghana a zangon karatu na shekarar 1999/2000 / Others
Yadda Christina Koch ta daga tutar Ghana a yayin tafiyarta zuwa Duniyar Wata
Christina Koch, ta ɗaga tutar Ghana yayin da suke tafiya a cikin jirgin sama jannati a matsayin wata sadaukarwa da kuma girmamawa ga ƙasar ta yankin Yammacin Afirka.

Christina Koch, wata 'yar sama jannati da ta yi karatu a Ghana, za ta kafa tarihi a matsayin mace ta farko da ta yi tafiya daga duniyarmu ta Earth zuwa duniyar Wata tare da tawagarta a aikin tafiyar jirgin sama jannati na Artemis II.

Ghana da sauran kasashen duniya sun jinjina mata da tawagarta baki daya.

Alakar Koch da kasar da ke Yammacin Afirka wani muhimmin ɓangare ne na labarinta. Ta shafe wasu lokuta a matsayin ɗalibar musayar ilimi a Jami'ar Ghana a zangon shekarar karatu tsakanin 1999/2000, inda ta karanta kimiyyar taurari tare da samun kanta da son al'adun Ghana.

Duk da kasancewarta a sararin samaniya, ba ta manta da ƙasar ba. Ta ɗaga tutar Ghana yayin da suke tafiya a cikin jirgin sama jannati a matsayin wata sadaukarwa da kuma girmamawa ga ƙasar ta yankin Yammacin Afirka.

'Yanayi mai ratsa zuciya'

Shugaban ƙasar Ghana John Mahama ya bayyana farin cikinsa kuma ya yi mata fatan nasara tare da tawagarta a tafiyar aikinsu na zuwa duniyar wata da kuma dawowa lafiya.

A cikin wata sanarwa da aka fitar ranar 9 ga Afrilu, Shugaba Mahama ya ce karamcin da Koch ta yi na ɗaga tutar ƙasar Ghana a sararin samaniya "yanayi ne mai ratsa zuciya ga kowane ɗan ƙasar Ghana".

Shugaba Mahama ya ƙara da cewa rayuwarta daga Jami’ar Ghana zuwa na gaba-gaba a cikin masu bincike a sararin samaniya ya zama "wani abin karfafa gwiwa sosai" ga kowane matashi ɗan ƙasar Ghana da Afirka.

Kazalika ya ce hakan tunatarwa ne na cewa cibiyoyin ilimi na ƙasar "suna ci gaba da samar da kuma tsara shugabannin duniya waɗanda ke kafa tahiri tare da kaiwa babban matsayi a rayuwa".

An haife ta a shekarar 1979 a jihar Michigan ta Amurka, rayuwar Koch zuwa sararin samaniya ta soma ne ta hanyar samun tushe mai ƙarfi a fannin karanta injiniyan lantarki da kimiyyar lissafi, inda ta sami digirinta na farko da na biyu daga Jami'ar Jihar North Carolina.

Tafiyar farko ta mata zalla zuwa sararin samaniya

Manyan ayyukan da 'yar sama jannatin ta yi sun haɗa da zaman kwanaki 328 a Tashar Sararin Samaniya ta Duniya, inda ta gudanar da bincike mai zurfi kuma ta shiga aikin tafiyar mata zalla zuwa sararin samaniya tsakanin 2019 da 2020.

A matsayinta na ƙwararriya a tawagar jirgin Artemis II, Koch na daga cikin mutanen da za su kafa tarihin zuwa duniyar Wata tare da gudanar da muhimman ayyukan bincike.

A yayin tafiyar kwanaki 10 da ta fara a ranar 1 ga Afrilu, 2026, Koch da abokan aikinta - Reid Wiseman, Victor Glover, da Jeremy Hansen - sun yi tafiyar mil 6,400 zuwa ga duniyar wata.

Wannan dai ita ce tafiyar ɗan adam ta farko zuwa duniyar wata tun bayan fiye da shekaru 50 jirgin Apollo ya kafa tarihi a shekarun 1970.

Rumbun Labarai
Nijeriya: An haramta wa 'yan ƙabilar Igbo naɗin sarautar gargajiya a ƙasashen waje
Nijeriya ta ƙwato kuraye biyu, beguwa da wasu tsuntsaye da ake ba wa kariya a wajen masu fasa-ƙwauri
Daga ƙasusuwa zuwa abin kwaɗayi: Orenge, abincin da ke sanya santi a Nairobi
Yadda A-Daidaita-Sahu na mata zalla ke sauya sufuri a jihar Kano ta Nijeriya
Kafafen sada zumunta na da alaƙa da raguwar farin ciki a faɗin Afirka da wasu yankuna - Rahoton 2026
Kuomboka: Ƙayatattun al'adun Masarautar Zambia mai shekara 300
Ƙalubalen sauyin yanayi a Afirka: Asarar rayuka, tafiyar ruwa da gidaje da rashin tabbas
An haifi wasu ‘yanbiyun gwaggwon biri da ke da wuyar samu karo na biyu a Congo DRC
Yadda raguwar kudin tallafi ke kai mutane kabari a Afirka
Yaya kaifin basira da fahimtar tausayi yake tsakanin giwaye?
Lailatul Qadri: Dare guda mai darajar watanni 1,000
Cutar kuturta a Afirka: Yanzu ne lokacin sauya lamarin
Mohbad: Taƙaddama game da ko marigayi mawaƙin Nijeriya shi ne uban ɗansa na asali
Mata da 'yanmata na cikin mafi munin bala'i da ƙasƙanci a Gaza - MDD
Azumi da Ciwon Suga: Shawarwarin ƙwararrun Lafiya ga Musulmai a watan Ramadan
An gano ƙwarangwal ɗin wata babbar dabbar dinosaur mai kama da tsuntsu a Hamadar Nijar
Yadda Harsuna 2,000 suka sa Afirka ta zama nahiya mafi yalwar lugga a duniya
Ramadan a Gaza: Falasɗinawa na kokawa kan yadda yaƙi ya hana su abubuwan da suka saba lokacin azumi
Cibiyar Al’adu ta Yunus Emre ta haɗa Turkiyya da Nijeriya ta hanyar fasaha
Yadda azumin Ramadan ke inganta lafiyar jiki