| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
Daruruwan Larabawa makiyaya 'yan kabilar Mahamid da Nijar ta kora sun isa Chadi
Gwamnatin Nijar na zargin ƙabilar Mahamid da samar wa ’yanta’addan Boko Haram da makamai da kuma tallafin kayan aiki da sufuri domin gudanar da ayyukansu a yankin.
Daruruwan Larabawa makiyaya 'yan kabilar Mahamid da Nijar ta kora sun isa Chadi
A makon da ya gabata, hukumomin yankin sun ce gwamnatin Nijar ta ba wa al’ummar Mahamid wa’adin zuwa ƙarshen wannan shekara domin ficewa daga ƙasar. / Others
 

Kimanin makiyaya Larabawa 800 daga ƙabilar Mahamid, waɗanda suka shafe shekaru da dama suna zaune a yankin kudu maso gabashin Nijar, sun isa Chadi bayan hukumomin Nijar sun umarce su da su bar ƙasar, kamar yadda gwamnatin Chadi ta bayyana a ranar Juma’a.

Gwamnatin Nijar na zargin ƙabilar Mahamid da samar wa ’yanta’addan Boko Haram da makamai da kuma tallafin kayan aiki da sufuri domin gudanar da ayyukansu a yankin.

A makon da ya gabata, hukumomin yankin sun ce gwamnatin Nijar ta ba wa al’ummar Mahamid wa’adin zuwa ƙarshen wannan shekara domin ficewa daga ƙasar.

Ministan Yaɗa Labarai na Chadi, Gassim Cherif Mahamat, ya ce: “A halin yanzu, mutane 800 sun isa cikin ƙasar Chadi, kuma ana sa ran wasu za su ƙara zuwa kafin ranar 31 ga Disamba, kamar yadda hukumomin Nijar suka umarta.”

“Wannan mataki na korar al’ummar ya fi kama da korar mutane daga ƙasarsu ta asali, maimakon kawai umartar su da su bar wani yanki. Muna nuna damuwarmu kan wannan mataki da ba ya nuna kyakkyawar mu’amala tsakanin ƙasashe,” kamar yadda ministan, wanda kuma shi ne kakakin gwamnatin Chadi ya bayyana.

Yankin Diffa, wanda shi ne babban wurin da makiyayan ke zaune, ya shafe fiye da shekaru goma yana fuskantar hare-haren ’yanta’addan Boko Haram da ɓangaren ƙungiyar Daesh da ke hamayya da ita.

A cikin ’yan watannin nan, al’ummar Mahamid sun fuskanci matakai daban-daban daga hukumomin Nijar.

Rukunin farko na makiyayan Mahamid sun isa Nijar a farkon shekarun 1970, bayan sun tsere daga mummunar fari da ya addabi yankin Abeche da ke gabashin Chadi, mahaifarsu.

Daga baya, wasu ƙungiyoyi sun biyo bayansu sakamakon rikice-rikicen da suka ɓarke a Chadi da maƙwabciyarta Sudan.

Sai dai ƙarancin wuraren kiwo da ruwa, tare da ƙaruwa da yawan dabbobi, musamman raƙuman da al’ummar Mahamid ke kiwo, sun jawo arangama tsakanin su da mazauna yankin, inda a wani lokacin har arangamar na kai ga rasa rayuka.

An ƙulla yarjejeniyoyin zaman lafiya daban-daban, ciki har da wadda aka cimma a shekarar 2018, amma har yanzu ba su yi nasarar rage tashin hankalin ba.