Watanni 26 da shida bayan kisan kiyashin da Isra'ila ta yi a Gaza, wani rikici cikin sirri na faruwa a tsakanin sojojin Isra'ila. Isra'ilawa da yawa sun fara fahimtar cewa wani abu a cikin sojoji yana afkuwa: rugujewar lafiyar kwakwalwa gaba ɗaya.
A cewar Ma'aikatar Tsaron Isra’ila, sama da sojoji 85,000 sun nemi maganin matsala a kwakwalwa da tunani tun daga watan Oktoban 2023, adadi mafi girma da aka taɓa samu a tarihin ƙasar.
Bayanai game da kashe kai a yanzu sun kai matsayi mafi girma a cikin shekaru 13. Tsakanin Janairun 2024 da Yulin 2025, aƙalla sojoji 279 sun yi ƙoƙarin kashe kansu, kuma da dama sun mutu.
Tun lokacin da aka fara kisan kiyashin a watan Oktoban 2023, sojojin Isra'ila sun kashe Falasɗinawa sama da 70,300, yawancinsu mata da yara kanana, inda suka kuma jikkata sama da mutane 171,000, a cewar hukumomin lafiya na Gaza.
A makon da ya gabata, wani jami'in tsaro daga Rundunar Givati ya mutu sakamakon kashe kansa bayan "matsananciyar damuwa ta kwakwalwa." Wani soja, mai shekaru 21 kacal, ya shaida wa 'yan majalisa cewa shiga kisan kare dangi a Gaza ya sa shi cikin mawuyacin hali, kuma yanzu ya zama "gawa mai tafiya".
Domin fahimtar dalilin da ya sa irin waɗannan labaran suka zama ruwan dare, masana ilimin halayyar ɗan adam suna ƙara koma wa ga manufar 'nadamar zalunci', wanda shi ne lalacewar da ke faruwa lokacin da wani ya ji ya ketare iyaka da ba zai iya warwarewa ba.
"Nadamar zalunci na nufin damuwa da ke tattare da fallasa ga ayyukan da ba su dace da halayya da ɗabi'a ba; a wannan karon, shi ne kisan kare dangi," a cewar masaniyar ilimin halayyar ɗan adam Asude Beyza Savas.
"Bincike kan aikin soja ya gano cewa abubuwan da suka faru masu tayar da hankali, kamar shiga yaƙi, suna taka muhimmiyar rawa wajen tunanin kashe kai a tsakanin mambobin soja," Savas ta fada wa TRT World.
"Idan muka yi duba na tsanaki sosai ga laifin, za mu ga cewa fuskantar abubuwan da ka iya nadamar aikata zalunci, musamman waɗanda suka shafi laifin da mutum ya yi da kansa, daga baya sai a samu ciwon damuwa na tsawon lokaci," in ji Savas.
Wannan yana haifar da janye wa daga al'umma, kuma ware kai abu ne da aka sani da ke haifar da kashe kai, in ji ta.
A lokacin zaman majalisar dokoki na baya-bayan nan a Knesset, sojojin Isra'ila sun zubar da tarin magungunan tabin hankali, har ma da opioids, a kan teburi, suna cewa, "Muna da tabin hankali, kuma abokanmu suna kashe kansu."
Mutane a yanar gizo ba su ja da baya ba. "Kashe wadanda ba su ji ba ba su gani ba na da illa ga tunanin ɗan adam," in ji wani mai amfani da X. Wani kuma ya ƙara da cewa: "Eh, jefa bama-bamai a kan jarirai abu ne mai illa ga lafiyarka."
Hakika, sojojin Isra'ila da yawa sun shiga Gaza da tabbacin rawar da suke takawa, amma wasu suna dawo wa ba tare da sun iya rayuwa da abin da suka gani ko suka yi ba. Kamar yadda matar wani soja da ya mutu sakamakon kashe kansa ta faɗa, "Ya mutu tun kafin ya mutu. Ransa ya mutu a Gaza."
Zuciya ta karye saboda tuna barnar da aka yi
A cewar kwararru, 'nadamar zalunci' da ke haifar da kashe kai a tsakanin sojojin Isra'ila ta ɗan bambanta da alamun tsoro na Matsalar Damuwa Bayan Tashin Hankali (PTSD).
Kwararrun sun bayyana wannan a matsayin abin da ke faruwa da zarar soja ya fahimci cewa ya shiga, kuma ya ba da dama, ko ya shaida ayyukan da suka yi karo da ka’idojin rayuwa da suka yi imani da su a baya.
Maimakon tunawa ko saka ido sosai, nadamar zalunci na bayyana a matsayin babban abin kunya, laifi da ƙyama ga karan kai. A wajen sojoji da yawa, wannan shi ne ainihin abin da ke faruwa a Gaza.
Lokacin da mutane suka ji sun ketare iyakokin halayyarsu mai kyau, sau da yawa suna fuskantar rikici mai zurfi na fahimta tsakanin ganin kansu a matsayin "masu aikata daidai" da kuma fahimtar shigar su ko haɗin gwiwa wajen lahanta wasu, a cewar Dr Ayse Sena Sezgin, malama a Sashen Nazarin Halayyar Dan Adam a Jami'ar Marmara.
"A tattare da nadamar zalunci, wasu hanyoyin fahimta da motsin rai suna taka rawa, ciki har da rashin jituwa ta fahimta, kebe kai, rikice-rikicen barci, damuwa, jarraba, tunanin kashe kai, rashin sanin ma'anar me aka aikata, da kuma tashin hankali na rayuwa," Sezgin ya shaida wa TRT World.
"Bayan shiga kai tsaye cikin tashin hankali, mutane na iya samun kansu cikin rashin jituwa tsakanin ɗora alhakin ga waɗanda suka ba da umarni da kuma ɗaukar alhakin da kansu.
Wannan matsala tana kawo babban laifi tare da kunya da nadama, wanda ke sa neman taimako ya fi yin wahala," in ji ta.
Savas ta ce wannan rushewar ita ce abin da ake iya faɗi game da tunanin mutum bayan shiga cikin ayyukan ta'addanci.
Ta hanyar shiga kisan kare dangi da kashe fararen hula, ta bayyana, sojoji suna fuskantar kunar zuci na kai tsaye da kuma na biyu na shaida shan wahalar wasu.
"Tuna me ya faru na shafar yanayin tunaninsu na yanzu kuma an nuna hasashen samun matakan damuwa na dogon lokaci, alamun zautuwa za su bulla daga baya, da lalacewar fahimtar kai wanda laifi da nadamar zalunci suka haifar."
Wannan tsari yana nuna abin da sojoji a ƙasa suka yarda da shi. Mutane da yawa suna bayyana lokutan da suka wargaza tunanin kansu.
Wani soja ya ba da labarin shiga wani gida da aka lalata ya ga gawarwakin yara biyu:
"Babu 'yan ta'adda a wurin... Na san duk yana kaina ne, cewa na yi haka. Ina son yin amai," an rawaito shi yana fadin hakan.
Masana sun ce kashe mutane, musamman fararen hula, na ɗaya daga cikin me ke janyo kashe kai tsakanin sojoji. Kuma idan wannan cutar ta yi yawa, ta ci gaba, kuma wani ɓangare na kisan kare dangi, 'nadamar zalunci' za ta ƙara tsananta.
Abin da ya ƙara dagula lamarin shi ne, sojoji da yawa suna cewa ana neman su musanta abin da suka gani.
Wasu ƙungiyoyin Yahudawa suna ci gaba da tura labarai kamar "Pallywood," wanda ke nufin Falasɗinawa sun shirya wa kansu wahala don su tausaya musu.
A wajen sojoji, wannan musantawar ya haifar da ƙarin rauni saboda sun dawo suna fahimtar abinda suka yi, sai kawai suka ga wata al'umma tana nace musu da cewa babu ɗaya daga cikin abubuwan da ya faru. Tunda kunya ba ta da inda za ta je, sai kawai ta shiga cikin lamarin.
"A wani bincike na dogon lokaci da aka yi kwanan nan kan tsaffin sojojin Isra'ila da aka sallama kwanan nan inda ake binciken laifi da yafe wa kai da ke da alaƙa da nadama, an gano cewa aikata abubuwan da za su iya cutar da ɗabi'a, musamman lokacin da soja da kansa ya aikata, an gano hakan ne laifin da ke da alaƙa janyo kashe kai," in ji Savas.
"Laifi da kunyar da ke da alaƙa da waɗannan ayyukan ƙetare haddi na haifar da rashin jituwa ta fahimta, yanayin rashin jin daɗi lokacin da mutum ke da ra’ayi masu karo da juna ko kuma lokacin da ayyukan mutum suka saɓa wa ƙa'idojinsu.
Ga shi, aikin da suka aikata ne, rashin iya daidaita wa da shi, da kuma jin laifi game da aikata shi."
"Wannan rashin jituwa a fahimta yana haifar danadamar zalunci da kuma zautuwar zuciya, waɗanda aka gano a matsayin hatsari da hasashen abubuwan da ke haifar da kashe kai," in ji ta.
Al’umma masu zuwa ba za su warke ba
Yayin da matsalar lafiyar kwakwalwa ke ƙara ta'azzara, sojojin Isra'ila na ci gaba da nuna suna da iko. Jami'ai sun yi nuni ga sabbin asibitoci, an tanadi ɗaruruwan jami'an lafiyar kwakwalwa, shirye-shiryen hana kashe kai, da kuma layukan waya na tallafi.
Amma babu ɗaya daga cikin su da ya canza gaskiyar cewa rugujewar tunani a cikin rundunonin ba za a iya fatan a yi watsi da su ba yayin da ake mayar da sojoji don aikata irin wannan tashin hankali.
Ɗan majalisar Knesset mai sassaucin ra'ayi Ofer Cassif ya kira wannan "annobar kashe kai" wanda za ta zama matsalar da babu makawa idan aka kawo ƙarshen yaƙin.
Idan aka yi la'akari na dogon lokaci, masanin ilimin halayyar ɗan adam Sezgin ya ce wannan tsari zai iya sake fasalta labaran zamantakewa, tsarin iyali, har ma da ilimi da siyasa ta hanyar jin aikata laifi na tsawon lokaci, kunya, da damuwar da ba a warware ba.
"Ba tare da tabbatar da cewa waɗanda ke da alhakin an hukunta su yadda ya kamata ba, ba zai yiwu a dawo da zaman lafiya da aminci a tsakanin jama'a ba, ko kuma a sake samun walwalar tunani a matakin daidaikun murane," in ji Sezgin.
Masaniyar ilimin halayyar ɗan adam Savas ta kuma lura cewa ba kamar nadama ta zahiri ba, nadamar zalunci ba ta ɓacewa.
"Damuwa ta biyu na iya taso wa daga jin labarin wani da abinda ya faru da su da mummunan halin da suka shiga. Wannan rugujewar ɗabi'a na shafar tsoffin sojoji da kuma na kusa da su ta hanyar nadamar da suka shiga," in ji Savas.
Ta ƙara da cewa bincike kan damuwa daga zamani zuwa zamani ta nuna cewa yaran da ke fama da damuwar bayan yaki galibi suna nuna alamun damuwa da rauni mai yawa. "Wannan yana nuna cewa rauni na iya zama na gado, ko kuma aƙalla yana da mummunan tasiri a tsawon lokaci."
Saboda haka, tasirin ya fi ƙarfin sojojin kansu. Isra'ila tana kan hanyar fitar da wani tsari wanda mutanen da suka dawo gida cikin ƙoshin lafiya amma suka yi nadamar zalunci a cikin zuciyarsu saboda abin da suka yi.
"A irin wannan yanayi, dukkan al'umma na iya fuskantar ƙaruwar rauni mai tsanani, da kuma babban baƙin ciki, rashin lafiya da damuwa, shan ƙwayoyi, rashin barci, da hatsarin kashe kai, wanda zai iya haifar da ƙaruwar laifuka," in ji Sezgin.
Sezgin ta bayyana cewa tasirin ilimin halin ɗan adam ya shafi ayyukan zamantakewa, gami da raguwar ma'aikata, rikice-rikicen iyali, da kuma ƙaruwar hatsarin rashin aikin yi.
Abin da ke faruwa a cikin sojojin Isra'ila shi ne asarar tunanin yaƙin da aka gina akan wahalar fararen hula. Ga dubban sojoji, rugujewar ta riga ta fara, kuma za ta biyo bayansu bayan yaƙin ya ƙare.















