A karo na biyu cikin kaka guda, Real Madrid za ta kara Benfica a wasan cike gurbi, don fayyace ƙungiyoyi 16 da za su je zagayen siri-ɗaya-ƙwale na gasar Zakarun Turai ta UEFA.
Benfica ta lallasa Madrid da ci 4-2 a birnin Lisbon na Portugal, a wani wasa da ya ƙayatar saboda gola ya ci ƙwallo ta 4 a mintin ƙarshe, sannan koci Jose Mourinho ya doke tsohuwar ƙungiyarsa.
Ana kallon maimaita haɗuwar a matsayin wata dama da Real Madrid za ta nemi ɗaukar fansa kan kunyatawar da aka mata. Madrid dai ita ce ta fi kowa suna a gasar saboda lashe kofin har sau 15.
Sai dai kamar yadda ɗanwasan gaban Madrid, Kylian Mbappe, ya faɗa, “Muna da ƙarin wasa biyu, kuma hakan da ciwo. Mun so mu samu lokaci a Fabrairu don inganta wasanmu, amma ga shi za mu buga wasannin cike gurbi.”
Sauran wasanni
A sauran wasanni da za a buga tsakanin ƙungiyoyin da suka gaza wucewa gaba kai-tsaye, Paris Saint-Germain mai riƙe da kofi za ta kara da maƙwabciyarta ta Faransa, Monaco.
Newcastle ta Ingila za ta kara da Qarabag ta Azerbaijan. Ban da Newcastle, duka ƙungiyoyin Ingila sun wuce gaba kai-tsaye: Arsenal, Chelsea, Liverpool, Manchester City, da Tottenham.
Ba ya tawagogin Ingila, sauran ƙungiyoyi uku da suka cika takwas da suka wuce zagayen gaba su ne, Barcelona, Bayern Munich da Sporting CP.
Sauran wasannin su ne: Galatasaray da Juventus, Bodo/Glimt da Inter, Club Brugge da Atletico Madrid, Borussia Dortmund da Atalanta, Olympiacos da Bayer Leverkusen.
Za a buga ƙafar farko ta wasanni a ranakun 17 da 18 ga Fabrairu, sai a buga ƙafa ta biyu mako guda bayan nan, a ranakun 24 da 25 ga Fabrairu.












