| Hausa
WASANNI
1 minti karatu
Atletico Madrid ta ce ta cim ma yarjejeniya da Atalanta kan ɗanwasan gaban Nijeriya Ademola Lookman
"Yarjejeniyar ta dogara ne a kan tabbatar da lafiyarsa da amincewa da kuma rattaɓa hannu kan kwantiraginsa,” in ji Atletico, ba tare da ƙarin haske ba.
Atletico Madrid ta ce ta cim ma yarjejeniya da Atalanta kan ɗanwasan gaban Nijeriya Ademola Lookman
Ademola Lookman ya buga wa Fulham da Leicester kafin ya koma Atalanta a shekarar 2022. / Reuters
2 Fabrairu 2026

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Atletico Madrid ta Sifaniya ta ce ta cim ma yarjejeniya da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Serie A, Atalanta, kan cinikin ɗanwasan gaban Nijeriya Ademola Lookman.

Kamfanin dillancin labaran AP ya ruwaito cewa Lookman yana Madrid domin sanya hannu a kwantiraginsa, in ji ƙungiyar ta Sifaniya ranar Lahadi.

"Yarjejeniyar ta dogara ne a kan tabbatar da lafiyarsa da amincewa da kuma rattaɓa hannu kan kwantiraginsa,” in ji Atletico, ba tare da ƙarin haske ba.

A ranar Litinin ne za a yi wa Lookman gwajin lafiya. Ɗanwasan mai shekara 28 ya buga wa Fulham da Leicester kafin ya koma Atalanta a shekarar 2022.

Ya kuma buga wasa a ƙungiyoyin Leipzig da Everton a baya. Lookman ya zura ƙwallaye uku a ragar abokan hamayyar Nijeriya a Gasar Cin Kofin Afirka ta shekarara 2025.

Atletico ita ce ta uku a teburin La Liga, maki tara bayan ƙungiyar Real Madrid da ke ta biyu a teburin kuma maki 10 a bayan Barcelona da ke kan gaba a teburin bayan wasanni 22.

Ƙungiyar za ta fafata da Club Brugge a wasan neman shiga Gasar Zakarun Turai daga baya a cikin wannan watan.