| Hausa
DUNIYA
2 minti karatu
An kona gini mai kama da masallaci a Arewacin Ireland a yayin da ‘yansanda ke gudanar da bincike
Ginin mai kama da Masallaci da aka girke bayan zanga-zangar adawa da 'yan gudun hijira ta baya-bayan nan, ya fuskanci suka daga 'yan siyasar da suke bayyana shi a matsayin barazana.
An kona gini mai kama da masallaci a Arewacin Ireland  a yayin da ‘yansanda ke gudanar da bincike
Butum-Butumin Masallacin na da hoton mutum a taga daya dauke da wani abu da yayi kama da wuka

An cinna wuta kan wani gini mai kama da Masallaci da aka girke a kusa da garin Belfast na Birtaniya a daren Alhamis kafin ‘yansanda su samu damar cire abinda suka bayyana a matsayin “Nuna tsana” wanda ‘yansiyasa a fadin kasar suka soka.

An kunna wuta a duk faɗin yankin Birtaniya a unguwannin da galibin mazaunansu masu biyayya ga darikar Furotesta ne a addinin Kirista a jajiberen ranar 12 ga Yuli don tunawa da nasarar William na Orange a kan Sarkin Katolika na Roman James a Yaƙin Boyne a 1690.

"Da a ce ba a kunna wuta ba, da 'yansanda sun tsare wurin kuma sun cire kayan da suke na muni inda suka kama shi a matsayin shaida. Laifukan ƙiyayya ba su da matsayi a cikin al'ummarmu kuma ba za a lamunce su ba," in ji Babban Sufeton 'Yan Sanda Norman Haslett a cikin wata sanarwa.

Ana sa ran wani mutum mai shekaru 56 da ake tuhuma da laifin tayar da hankali zai gurfana a gaban kotu ranar Jumma'a.

‘Aikin yin barazana’

Ministar Birtaniya a Arewacin Ireland, Hilary Benn, ta bayyana lamarin a ranar Alhamis a matsayin "barazanar matsorata".

Hotunan nuna kyamar bakin haure a wasu lokutan sun maye gurbin alamu da hotunan 'yan siyasar Katolika na Ireland da kuma taken kin jinin Katolika da aka saba sanyawa a kan wasu wutar da aka cinna.

An cinna wuta kan wani abu mai kama da 'yan gudun hijira a cikin kwale-kwale a bara a daidai wannan wuri a Moygashel, kilomita 65 yamma da Belfast. Hakan kuma ya biyo bayan lokacin tashin hankali inda aka kai hari kan gidajen bakin haure.

Masu zanga-zanga sun kai hari kan gidaje da kasuwancin tsirarun kabilu cikin tarzoma a watan da ya gabata bayan wani bidiyo da aka watsa da ya nuna yadda aka soka wa wani mutum wuka a ciki.

Masallacin na da hoton mutum a taga daya dauke da wani abu da yayi kama da wuka. Tutocin da ke kasa sun rubuta "kula da iyakokinmu" da kuma "kawo karshen barazanar tsattsauran ra'ayi na Musulunci".