| Hausa
TURKIYYA
2 minti karatu
Fidan na Turkiyya ya gargaɗi Amurka kan kai wa Iran hari, ya ce Tehran a shirye take ta tattauna
Babban jami’in diflomasiyyar Turkiyya ya shawarci jami’an Amurka da su magance matsalolinsu da Iran nan da nan maimakon neman wata faffadar yarjejeniya.
Fidan na Turkiyya ya gargaɗi Amurka kan kai wa Iran hari, ya ce Tehran a shirye take ta tattauna
Babban jami'in diflomasiyyar na Turkiyya ya yi kira ga amrka da ta warware matsalolinta da Iran cikin hanzari. / Reuters / Reuters
29 Janairu 2026

Ministan Harkokin Waje na Turkiyya Hakan Fidan ya yi gargadin cewa harin da Amurka za ta kai wa Iran zai zama "kuskure", yana mai kira ga Washington da Tehran da su warware taƙaddamar da ke tsakaninsu ta hanyar diflomasiyya.

A wata hira da ya yi da Al Jazeera, Fidan a ranar Laraba ya yi kira da a hada kai a yankin yayin da Amurka ke tura sojoji da kayan yaki zuwa Gabas ta Tsakiya a daidai lokacin da ake kara samun rikici tsakaninta da Iran.

"Ba daidai ba ne a sake fara yakin."

Duk da karuwar cacar baki a tsakanin kasashen biyu, Fidan ya jaddada cewa har yanzu ana iya cim ma matsaya ta hanyar diflomasiyya.

"Iran a shirye take ta sake tattaunawa kan batun nukiliya," in ji Fidan.

Jami'in diflomasiyyar Turkiyya ya shawarci jami'an Amurka da su magance matsalolin da Iran ke fuskanta a hankali maimakon neman yarjejeniya mai zurfi.

"Shawarata ga abokan Amurka ita ce a rufe batutuwan daya bayan daya da Iran. A fara da batun makaman nukiliya, a rufe batun, sannan a tafi ga sauran," in ji shi.

"Idan ka sanya su a waje guda baki daya, dukkan su, zai yi wa abokanmu na Iran wahala su yi nazari a kan su, kuma su aiwatar da su tare da shawo kan batutuwan."

"Kuma wani lokacin, yana iya zama abin kunya a gare su. Zai yi musu wahala su yi wa kansu bayani, har ma da shugabanci."

Ya kuma ce Iran za ta iya zama "wuri mai kyau" a cikin tsarin yanki, amma dole ne ta gina amintaka da ƙasashe maƙwabta.

"Su (Iraniyawa) suna buƙatar ƙirƙirar aminci a yankin," in ji shi.

"Suna buƙatar mayar da hankali ga yadda ƙasashen yankin ke ɗaukarsu, domin ba za su je ko ina ba; ba za mu je ko'ina ba."

Fidan ya jaddada cewa duk da aƙidu da ƙungiyoyi daban-daban, dole ne ƙasashen yankin su yi aiki tare a cikin tsarin ƙasa-ƙasa.