| Hausa
WASANNI
2 minti karatu
Mourinho ya bai wa Kocin Real Madrid haƙuri bayan Benfica ta doke Madrid a Gasar Zakarun Turai
Mourinho dai tsohon kocin Real Madrid ne, kuma ya amsa cewa sai daga baya ya fahimci cewa Benfica na buƙatar cin Madrid ƙarin ƙwallo don ci gaba da kasancewa a gasar ta Zakarun Turai.
Mourinho ya bai wa Kocin Real Madrid haƙuri bayan Benfica ta doke Madrid a Gasar Zakarun Turai
Jose Mourinho tsohon kocin Real Madrid ne / AP
29 Janairu 2026

Yayin da aka kammala zagayen rukuni na Gasar Zakarun Turai a maraicen Laraba, wani wasa da ya ɗauki hankali shi ne na tsakanin Benfica ta Portugal, da Real Madrid ta Sifaniya.

Benfica ta doke Madrid da ci 4-2 a wasan da ya fayyace ƙungiyoyin da suka samu wucewa zagayen gaba kai-tsaye, da waɗanda za su buga wasannin cike gurbi, da waɗanda suka fice daga gasar.

Nasarar Benfica ta ƙayatar saboda golanta, Anatoliy Trubin, ya baro ragarsa don ba da taimako, sannan ya ci ƙwallo ta huɗu da-ka a minti na 98 na ƙarshen wasan.

Wannan nasarar ta ba wa Benfica damar ƙarewa a mataki na 24 a teburin gasar, da samun damar buga wasannin cike gurbi, sakamakon tazarar yawan ƙwallaye ta take da shi.

Sai dai ita kuma Madrid, ta faɗo daga jerin ƙungiyoyi takwas na saman tebur, waɗanda suke wuce zagaye na gaba kai-tsaye. Kuma yanzu ita ma sai ta buga wasan cike gurbi kafin matsawa gaba.

Neman ƙarin ƙwallo

Yadda Benfica ta samu tsira cikin mintin ƙarshe ya haifar da gagarumar murna ga ‘yanawasa da magoya bayan ƙungiyar, ciki har da kocinsu Jose Mourinho.

Daga bisani, Mourinho ya bayyana wa manema labarai cewa sai da ya je ya samu kocin Real Madrid, Alvaro Arbeloa, ya ba shi haƙuri saboda irin murnar da ya yi, wadda ka iya zama cin mutunci ga masoya Madrid.

Mourinho dai tsohon kocin Real Madrid ne, kuma ya amsa cewa sai daga baya ya fahimci cewa Benfica na buƙatar cin Real Madrid ƙarin ƙwallo don ci gaba da kasancewa a gasar Zakarun Turai.

Haka nan Mourinho ya ce ba shi da niyyar wulaƙanta Madrid, “Na ba da haƙuri kan yadda na yi murna, amma Álvaro masanin ƙwallo ne kuma ya fahimci cewa a irin wannan yanayi zuciya za ta iya ɗaukar mutum.

“Na sha ci da faɗuwa wasa da dama, amma ban taɓa lashe wasa inda gola ya ci ƙwallo a mintin ƙarshe ba. Da na ɗauka na ga komai a ƙwallo, amma a ƙarshe ashe ban gama gani ba.”