Yadda Gasar AFCON za ta zama bukukuwan al'adun Afirka a Morocco
AFCON 2025 Morocco / CAFonline
Yadda Gasar AFCON za ta zama bukukuwan al'adun Afirka a Morocco
Baya ga buga ƙwallon ƙafa, Gasar AFCON ta zama wani fage da ake bikin nuna mabambantan al'adu da kaɗe-kaɗen al'ummomin Afirka.
kwana ɗaya baya

Kwanaki kaɗan ne suka rage a ƙaddamar da gasar kofin ƙwallon ƙafa na ƙasashen Afirka, AFCON 2025 a Morocco, wadda ƙasa ce mai tarihi da kuma yalwar ala’adu.

Wannan ne karo na biyu da Morocco ke ɗaukar nauyin wannan gasa, tun bayan da ta yi hakan a 1988.

A wannan karo gasar AFCON 2025 ta haɗo ƙasashe 24 daga duka yankunan Afirka, inda za su nuna ƙwarewarsu a fagen ƙwallo, tare da baje kolin al’adunsu.

A wurare tara za a gudanar da shagulgulan gasar cikin birane shida, wato Rabat, Casablanca, Marrakech, Fès, Tangier da Agadir, waɗanda za su bai wa baƙi damar ziyartar yankunan ƙasar.

Babban birnin ƙasar, Rabat yana da tituna na zamani da wuraren tarihi, yayin da birnin Casablanca yake da wuararen more rayuwa da ababen tarihi.

Birnin Tangier yana da yankuna masu cike da tasirin tekunan Bahar Rum da na Atlantic. Shi kuma Agadir yana bakin teku.

Da ma dai, baya ga buga ƙwallon ƙafa, gasar AFCON ta zamo wani fage da ake bikin nuna mabambantan al'adu da kaɗe-kaɗen al'ummomin Afirka.

Shagulgulan al’adu

Dodon gasar sunansa “ASSAD” wanda ke nufin zaki a Larabci. Kuma yana nuni da ƙarfi, alfahari, da kuma tushen ala’adu waɗanda suka haɗa Morocco da nahiyar Afirka.

Za a buɗe wuraren kallon wasanni a wajen filayen wasa a cikin ƙasar. Masoya ƙwallo da ba su shiga filin wasa ba, ko kuma ba sa garin da ake wasan, za su je wuraren don kallo a talabijin.

A wuraren za a gudanar da kaɗe-kaɗe da raye-raye don nishaɗantar da baƙi da ‘yankasa. Za kuma a samu abincin gargajiyar ƙasar Morocco, da wuraren buga ƙwallon nishaɗi.

Ƙasashe 24 ne za su fafata don neman ɗaukar kofin, inda kowace ƙasa za ta nuna gwanintarta a fagen ƙwallo, tare da magoya bayansu masu harsuna da al’adu daban-daban.

Haka ma a filayen wasannin gasar, ‘yanwasa da mahalarta za su samu nau’ukan abinci na ƙasar Morocco da ma na sauran ƙasashen Afirka.

Tuni dai baƙi daga Afirka da ma sauran ƙasashen duniya suka fara hallara a Morocco don jiran ranar Lahadi 21 ga Disamba da za a yi bikin buɗe gasar da za ta ƙare ranar 18 ga Janairun 2026.