Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-un ya sa ido a lokacin da aka gudanar da gwaje-gwajen makami mai linzami mai iya ɗaukar nukiliya da wasu makamai a cikin jirgin ruwan yaƙin ƙasar mai nauyin tan 5,000 mai suna Kang Kong, kamar yadda kafar watsa labarai ta ƙasar ta tabbatar a daidai lokacin da Pyongyang ɗin ke ƙoƙarin samar da rundunar sojin ruwa mai amfani da nukiliya
Kamfanin Dillancin Labarai na Koriya ta Arewa (KCNA) ya ce taron na ranar Jumma'a ya haɗa da gwajin makami mai linzami, bindigar babban jirgin yaƙin da igwa-igwa masu sarrafa kansu, kazalika da gwaje-gwajen tsarin yaƙin zamani.
Bayan kallon gwaje-gwajen daga bakin teku, Kim ya umarci jami'ai da su kammala gwaje-gwajen jirgin kuma su saka shi cikin ayyukan soja cikin watanni biyu, in ji hukumar labarai ta gwamnatin ƙasar.
Faɗaɗa rundunar ruwa
Wadannan gwaje-gwajen sun biyo bayan yadda Koriya ta Arewa ta ƙaddamar da jirgin yaƙinta na farko mai nauyin tan 5,000 a watan Yuni samfurin Choe Hyon, wani muhimmin mataki da Kim ya yi bikin alfarma inda ya ce makaman nukiliya a rundunar ruwansa suna tafiya yadda aka tsara.
Bayan shekaru ana ba da fifiko ga haɓaka makaman nukiliya, Kim ya ƙara mayar da hankali kan sojin ruwansa, ciki har da gina jirgin ƙarƙashin ruwa mai amfani da makamashin nukiliya. A yayin fayyace manufofinsa na soja na shekaru biyar a taron Jam'iyyar Ma'aikata na watan Fabrairu, Kim ya kuma nemi a yi makamai masu linzami masu zuwa nahiyoyi na jiragen ruwa na ƙarƙashin ruwa.
Taimakon ƙasashen waje
Koriya ta Arewa ta fara bayyana Choe Hyon a watan Afrilun 2025, wanda Kim ya nuna a matsayin muhimmin mataki wajen faɗaɗa ikon aiki na sojanta da ƙarfafa damar kai farmaki na gaba.
KCNA ta ce jirgin yakin na da na'urori daban-daban, ciki har da makaman kakkaɓo jiragen sama da nutsar da na ruwa, da kuma ƙarfin harba makamai masu linzami da ke ɗauke da nukiliya.
An bayyana Kang Kon wata guda bayan Choe Hyon a watan Mayun 2025, sai dai jirgin ya lalace a wajen wata ƙaddamarwa wadda aka samu matsala a arewacin tashar arewa ta Chongjin, abin da ya jawo fushin Kim.
Sannan ƙasar ta ce an sake ƙaddamar da jirgin a watan Yuni bayan gyare-gyare, amma masana daga waje sun yi tambaya kan ko gaske jirgin ya shirya shiga ayyukan soja.
Kim ya kuma nemi a gina sabbin jiragen yaki biyu masu nauyin tan 5,000 a kowace shekara a tsawon shekaru biyar masu zuwa, tare da samar da wani babban jirgin yaki mai tan 10,000.










