| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
Isra'ila ta kashe dala miliyan 46.5 wajen ƙoƙarin sa AI ya yaɗa ra'ayoyinta kan yaƙin Gaza
Rahoton ya ce wasu shafukan kamar Allyvia.org, FactSignal.org da Paxpoint.org sun riƙa kare matakan Isra'ila a Gaza, suna ƙalubalantar zarge-zargen da ake yi mata tare da gabatar da ra'ayoyin da ke goyon bayanta.
Isra'ila ta kashe dala miliyan 46.5 wajen ƙoƙarin sa AI ya yaɗa ra'ayoyinta kan yaƙin Gaza
Isra'ila ta kashe dala miliyan 46.5 wajen ƙoƙarin sa AI ya yaɗa ra'ayoyinta kan yaƙin Gaza / Reuters

Wani rahoto da Drop Site News ya wallafa ya yi zargin cewa Isra'ila ta kashe dala miliyan 46.5 wajen gudanar da wani kamfen na yaɗa bayanai ta intanet da nufin tasiri kan yadda tsarin basirar wucin gadi (AI) ke amsa tambayoyi game da yaƙin Gaza.

Rahoton ya ce Brad Parscale, tsohon manajan yakin neman zaɓen Shugaban Amurka Donald Trump, da kamfaninsa Clock Tower X, sun ƙirƙiri wata cibiyar shafukan intanet ƙarƙashin wannan kwangila domin yaɗa ra'ayoyin da ke goyon bayan Isra'ila da kuma yin tasiri kan a shafukan AI kamar ChatGPT, Claude, Gemini da Perplexity.

A cewar rahoton, an wallafa daruruwan makaloli a waɗannan shafukan intanet kan yaƙin Gaza, hare-haren sojin Isra'ila da dangantakar Amurka da Isra'ila, da nufin su shiga sakamakon binciken injunan neman bayanai kuma tsarin AI ya yi amfani da su wajen samar da amsoshi.

Rahoton ya ce wasu shafukan kamar Allyvia.org, FactSignal.org da Paxpoint.org sun riƙa kare matakan Isra'ila a Gaza, suna ƙalubalantar zarge-zargen da ake yi mata tare da gabatar da ra'ayoyin da ke goyon bayanta.

Drop Site News ya kuma ce an riga an samu wasu tsarin AI da suka fara ambaton waɗannan shafukan a cikin amsoshinsu, yayin da aka ce bayanan sun shiga rumbun bayanan Common Crawl, wanda ake amfani da shi sosai wajen horar da manyan tsarin AI.

Masana yaƙi da yaɗa bayanan ƙarya sun shaida wa rahoton cewa irin wannan dabara na iya yin tasiri saboda tsarin AI kan haɗa ra'ayoyi daga mabambantan tushe yayin amsa tambayoyi.

Rahoton ya kuma yi nuni da cewa goyon bayan jama'a ga Isra'ila a Amurka ya ragu sosai tun bayan fara yaƙin Gaza, wanda ya yi sanadin mutuwar fiye da Falasdinawa 73,000, ciki har da raguwar goyon baya a tsakanin wasu ƙungiyoyin da a baya ake ɗauka a matsayin manyan magoya bayan Isra'ila.