NIJERIYA
2 minti karatu
Obasanjo ya musanta neman wa’adi na uku, ya ce da ya ga dama da ya samu
“Ni ba wawa ba ne. Da a ce ina son wa’adi na uku, na san yadda zan yi na nema. Kuma babu wani ɗan Nijeriya, mai rai ko matacce, da zai ce na kira shi na gaya masa ina son wa’adi na uku,” in ji tsohon shugaban ƙasar.
Obasanjo ya musanta neman wa’adi na uku, ya ce da ya ga dama da ya samu
Obasanjo ya mulki Nijeriya daga 1976 zuwa 1979, sannan ya sake mulkarta daga 1999 zuwa 2007 / Others
10 awanni baya

Tsohon Shugaban Nijeriya Olusegun Obasanjo ya karyata zargin da aka jima ana yi masa kan cewa ya taɓa neman tsawaita wa’adin mulkinsa, inda ya jaddada cewa bai taɓa neman wa’adi na uku ba.

Ya bayyana haka ne a yayin wani taro na Democracy Dialogue da Gidauniyar Goodluck Jonathan ta shirya a Accra, Ghana.

Obasanjon ya ce babu wani ɗan Nijeriya, mai rai ko matacce, da zai iya cewa gaskata cewa ya taɓa roƙon goyon baya domin neman wa’adi na uku.

“Ni ba wawa ba ne. Da a ce ina son wa’adi na uku, na san yadda zan yi na nema. Kuma babu wani ɗan Nijeriya, mai rai ko matacce, da zai ce na kira shi na gaya masa ina son wa’adi na uku,” in ji tsohon shugaban ƙasar.

Obasanjo ya jaddada cewa a zamanin mulkinsa ya nuna ƙwarewarsa wajen cim ma manufofin ƙasa da ke da wuyar cimmawa, inda ya kawo misalin yadda Nijeriya ta samu afuwar bashi a lokacin mulkinsa a matsayin babban ƙalubale fiye da neman wa’adi na uku.

“Na kan faɗa musu cewa idan na iya samun afuwar bashi, wanda ya fi wahalar samu fiye da wa’adi na uku, to da ina so na samu wa’adi na uku, da na samu shi ma,” in ji shi.

Ya kuma gargaɗi shugabanni masu zama a kujerar mulki fiye da wa’adinsu, inda ya jaddada cewa imani da cewa mutum ba za a iya rayuwa ba sai da shi “laifi ne a wurin ubangiji.”

Olusegun Obasanjo, wanda tsohon soja ne ya fara mulkar Nijeriya daga shekarar 1976 inda ya miƙa mulki ga gwamnati farar hula a 1979.
Daga baya ya dawo a matsayin shugaban ƙasa da aka zaɓa ta hanyar dimokuraɗiyya daga 1999 zuwa 2007, bayan sojoji sun sake miƙia mulki ga farar hula.

Obasanjo ya taka muhimmiyar rawa wajen gyaran tattalin arziki, sauye-sauyen siyasa, da kuma ƙarfafa matsayi da mutuncin Nijeriya a harkokin ƙasa da ƙasa.