| Hausa
TURKIYYA
3 minti karatu
Yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Rasha da Ukraine za ta tsara makomar Turai: Fidan na Turkiyya
Ministan harkokin wajen Turkiyya Hakan Fidan ya ce ƙasarsa na da yaƙinin cewa Rasha da Ukraine za su cim ma matsayar da ta dace nan ba da jimawa ba.
Yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Rasha da Ukraine za ta tsara makomar Turai: Fidan na Turkiyya
Fidan ya tattauna kan ƙoƙarin kawo ƙarshen yaƙin da ke tsakanin Ukraine da Rasha. / AA
15 awanni baya

Ministan harkokin wajen Turkiyya Hakan Fidan, wanda ya halarci taron ministocin harkokin waje na ƙurgiyar NATO a Brussels, ya ce babu wani wuri mafi dacewa don tattaunawar zaman lafiya tsakanin Rasha da Ukraine fiye da Turkiyya.

"Mun tabbatar da hakan ta hanyar tarurrukan da muka gudanar har sau uku a Istanbul a bara lokacin bazara, inda muka karɓi baƙuncin tarurrukan. Ɓangarorin sun tafi cikin farin ciki," a cewar ministan a wata hira da TRT Haber da Anadolu suka yi da shi a ranar Laraba.

A jawabin da ya gabatar bayan tattaunawa da takwarorinsa na EU da NATO, Fidan ya ce tattaunawar ta mayar da hankali sosai kan yaƙin Rasha da Ukraine da neman tsarin zaman lafiya mai ɗorewa, da kuma batutuwan da suka shafi yankin inda Turkiyya ke taka muhimmiyar rawa.

Fidan ya ce yana ci gaba da fatan alheri game da tsarin zaman lafiya tsakanin Rasha da Ukraine.

"Abu mafi mahimmanci shi ne kada a bar teburin tattaunawa," in ji shi.

"Idan aka zauna da niyyar sulhu, daga ƙarshe za a cim ma yarjejeniya."

Ya ce, wakilin Amurka da ke shiga tsakani Steve Witkoff "yana da damar da ake buƙata" ta taimakawa a ci gaba da tattaunawa.

'Matsayar da ta dace'

Turkiyya na da yaƙinin cewa Rasha da Ukraine za su bayyana matsayar da ta dace nan ba da jimawa ba, in ji Fidan.

"Rasha tana da kyakkyawan hali," in ji shi. "Ina ganin ita ma Ukraine za ta bayyana nata nan ba da jimawa ba."

Fidan ya jadadda cewa duk wata yarjejeniyar da aka cim ma za ta tsara makomar Turai, ba wai kawai ƙarshen yaƙin ba.

"Kowa na ƙoƙarin tantance haɗura da kuma ribar da ke ciki,’’ in ji shi.

A irin wannan tirka-tirkar yanayin da ake ciki, fayyace manufofi da kuma mayar da su kan ɓangarorin na da matuƙar mahimmanci."

Hare-hare a Bahar Aswad

Kazalika, Fidan ya taɓo batun hare-haren da aka kai kwanan nan kan jiragen ruwa na kasuwanci kusa da gabar Bahar Aswad na Turkiyya.

Ya ce Turkiyya da Romania da Bulgaria duk sun kafa wata ƙungiya ta sintiri don yaƙi da masu satar ma'adinai da inganta tsaron teku, kana tuni sojojin ruwa suka ba da haɗin kai.

‘‘Hare-haren da aka kai kwanan nan sun nuna yadda gargaɗinmu suka yi tasiri,’’ in ji shi.

"Yanayin yaƙin na ɗaɗa faɗaɗa, kuma hakan na da haɗari sosai."

Dangantakar ƙungiyar EU

Fidan ya ce, dangantakar Turkiyya da kusan dukkan ƙasashen EU na ci gaba da bunƙasa, sai dai ya yi gargaɗin cewa ayyukan gwamnatin Cyprus ta Girka na ci gaba da kawo cikas ga haɗin gwiwar.

‘‘Duk wanda na yi magana da shi, zai sun yi korafi game da Gwamnatin Cyprus ta Girka,’’ in ji shi.

"Wani gungun mutane sun babakere da haɗin gwiwa tsakanin Turkiyya da Tarayyar Turai, wani al’amari da ya shafi makomar mutane fiye da miliyan 400.’’

Ya jadadda cewa,Turkiyya amintacciyar abokiyar hulɗa ce, mai adalci, wadda ke da cibiyoyi masu ƙarfi da maban-bantan al’umma da kuma kamfanonin daban-daban masu zaman kansu.

Cire shingen siyasa, a cewarsa yana da matukar mahimmanci ga dangantakar EU da Turkiyya don iya cim ma manufarsu.