| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
Hukumar Kwastam ta Jamhuriyar Nijar ta ƙwace nakiya 8,567
Aikin kamen, wanda Laftanar Kanal Fatimata Salifou Marafa, shugabar ofishin ta jagoranta, ya daƙile shigar da miyagun ababen fashewa cikin Nijar, lamarin da ya taƙaita isar irin waɗannan makamai ga ‘yanbindiga da ƙungiyoyin masu aikata laifuka.
Hukumar Kwastam ta Jamhuriyar Nijar ta ƙwace nakiya 8,567
Wannan ba shi ne karon farko da aka ƙwace miyagun ƙwayoyi ba a Nijar tun farkon shekarar 2025 / Garde Nationale
17 awanni baya

Jami’an hukumar kwastam a Jamhuriyar Nijar sun ƙwace nakiya mai tarin yawa da wasu masu laifi suka yi safararta yayin da ƙasar ke ci gaba da fama da rashin tsaro sakamakon hare-hare na ƙungiyoyin ‘yanta’adda a ƙasar da maƙwabtanta irin su Mali da Burkina Faso.

Ofishin hukumar hana fasa-ƙaurin Nijar da ke kan hanyar Yamai ya ƙwace sandunan nakiya 8,567 da aka ɓoye a cikin wasu kayayyakin da aka shiga da su ƙasar daga ƙasashen ƙetare, in ji darakta janar na hukumar kwastam ta Nijar. Wannan shi ne babban kame na biyu da hukumar ta yi tuna farkon shekarar 2025.

Aikin kamen, wanda Laftanar Kanal Fatimata Salifou Marafa, shugabar ofishin ta jagoranta, ya daƙile shigar da waɗannan miyagun ababen fashewa cikin ƙasar, lamarin da ya taƙaita isar irin waɗannan makamai ga ‘yanbindiga da ƙungiyoyin masu aikata laifuka.

Kamar Mali da Burkina Faso, Nijar tana fama da hare-hare daga ƙungiyoyi masu iƙirarin jihadi da ke da alaƙa da Al-Qaeda da kuma ƙungiyar IS.

Rashin tsaron da ƙasar ke fama da shi na cikin dalilan da aka bayar na juyin mulkin da ya kawo Janar Abdourahamane Tiani kan karagar mulki a shekarara 2023.  Ƙasashen uku dai sun kafa ƙungiyar AES ta ƙasashen Sahel domin haɗa kai wajen yaƙar ta’addanci.

A lokacin gabatar da ababen da aka ƙwacen, Kanar Rabiou Gouzaye, daraktan bincike na hukumar kwastam, wanda ya wakilci darakta janar ta hukumar, ya yaba wa jami’an bisa nuna ƙarewarsu. Ya jaddada muhimmiyar rawar da hukumar take takawa wajen yaƙar fataucin miyagun ƙwayoyi a yankin AES.