| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Majalisar Tattalin Arzikin Nijeriya ta amince da N100bn don gyara cibiyoyin horas da 'yansanda
An ɗauki wannan matakin ne a taron majalisar na 154 inda majalisar ta amince domin gyara cibiyoyin horas da ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro a faɗin ƙasar.
Majalisar Tattalin Arzikin Nijeriya ta amince da N100bn don gyara cibiyoyin horas da 'yansanda
Taron NEC / Kashim Shettima
13 awanni baya

Majalisar Tattalin Arziki ta Nijeriya (NEC) ta amince da naira biliyan 100, domin gyaran cibiyoyin horas da ‘yansanda da sauran hukumomin tsaro a faɗin ƙasar.

An ɗauki wannan matakin ne a taron majalisar na 154, wanda aka gudanar ta intanet a ranar Laraba, bayan gabatar da rahoton kwamitin wucin-gadi da aka kafa domin tantance halin da cibiyoyin horaswa na jami’an tsaro ke ciki.

Majalisar ta kuma amince da N2.6 biliyan domin biyan kudin masu ba da shawara kan aikin.

Sai dai duka waɗannan kuɗaɗen da aka amince sai sun jira amincewar shugaban ƙasa kafin a fitar da su.

Tun a taron NEC na 152 a watan Oktoba Shugaba Tinubu ya bayar da shawarar fara gagarumin gyara da sabunta cibiyoyin horaswa na jami’an tsaro a fadin ƙasa.

Shugaban kwamitin kuma Gwamnan Jihar Enugu, Peter Mbah, ya bayyana cewa yawancin cibiyoyin suna cikin mawuyacin hali, suna kuma bukatar a gyara su a cikin gaggawa.

Bayan gabatar da rahotonsa, Shugaban Majalisar Tattalin Arikin Ƙasa kuma Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya tabbatar da kudirin gwamnatin tarayya na magance matsalar, tare da jaddada buƙatar ganin sauye-sauye suna haifar da sakamako kai tsaye ga ‘yan kasa.

Shettima ya yi kira ga gwamnonin jihohi su tabbatar da cewa sauye-sauyen tattalin arzikin jihohinsu suna haifar da ingantuwar rayuwar jama’a, yana mai jaddada cewa ana auna sakamakon da gwamnati ta samar ba wai alƙawura ba.

Nijeriya ta samu raguwa da kashi 39 a cutar Polio

Gwamnan Jihar Gombe, Inuwa Yahaya, wanda ke jagorantar Kwamitin NEC kan kawar da cutar shan inna, ya bayyana cewa zuwa mako na 47, Nijeriya ta samu rahotanni 73 na wani nau’in polio da ke yawo na cVPV2, wanda ke nuna raguwar kashi 39 daga rahotanni 119 da aka samu a lokaci iri ɗaya a 2024.

Ya ce jihohi shida ne suka fi dauke da mafi yawan masu cutar, ciki har da Sokoto mai 23, Zamfara (9), Kebbi (7), Gombe (2), Kano (3), da Katsina (2).

Yahaya ya kuma bayyana ci gaba mai kyau a Kano da Katsina, inda aka samu raguwar 94% da 88%.

Majalisar ta bukaci Gwamnatocin jihohi su kara hadin gwiwa da jami’an tsaro domin samar da kariya da damar shiga ga tawagar rigakafi, musamman a yankunan da ke fama da matsalar tsaro.