Ka yi tunanin wata duniya inda mutane za su iya noma abinci a kan Wata ko ma a duniyar Mars. Kama yake da labarin kimiyya mai ban al'ajabi. Amma Sannu a hankali hakan ya soma zama gaskiya. A cikin wannan shirin, za mu lalubo wasu muhimman bincike da za su iya taimaka wa mutane su zauna har ma su iya yin noma a wasu duniyoyin.
Masana kimiyya na Turkiyya suna kan gudanar da gwaje-gwaje a duniya da kuma sararin samaniya kan wata shuka mai suna Schrenkiellaparvula. Wannan shukar na iya zama muhimmin mabudi wajen noma abinci a sararin samaniya. Bari mu duba yadda za a iya yin hakan.
