31 Oktoba 2025
Kudi, wato takardar kudi, kwandala da kwabo, sule da sisi, taro da fam, wuri da
ahu, dala da euro, dirhami da zinare, sefa da naira, har kudin dijital da kirifto,
dukkansu wani al’amari ne da yake da dogon tarihi a fannin samuwa, da karbuwa,
da sassauyawa.
Masana tattalin arziki sun ce kudi shi ne duk wani abu da ke taskace kima ko
kadara, kuma wanda al’umma suka amince da shi a matsayin abin musaya, domin
saye ko sayar da haja, ko kuma biyan bashi ko hakki.

