Aljeriya ta buɗe masallacin da ya fi kowanne girma a Afirka: Katafaren Masallacin Algiers

Aljeriya ta buɗe masallacin da ya fi kowanne girma a Afirka: Katafaren Masallacin Algiers

An yi bukukuwan buɗe katafaren masallaci a Aljeriya, wanda yake shirin karɓar baƙuncin masu ibada a cikin watan azumin Ramadana.
Wannan hoton ya nuna babban masallacin na birnin Algiers, wanda aka fi sani a kasar da sunan Masallacn Juma'ar Jaza'ir, a tsakiyar babban birnin kasar.

Aljeriya ta ƙaddamar da masallaci mafi girma a nahiyar Afirka a Gaɓar Tekun Mediterrenean, lamarin da ya kawo ƙarshen jinkirin da ke da alaƙa da siyasa da aka yi ta samu da kuma tsadar rayuwa bayan shafe shekaru.

Bikin buɗe masallacin a ranar Lahadi zai jagoranci Musulmi zuwa ga "kyakkyawar hanya madaidaiciya," in ji Ali Mohamed Salabi, Babban Sakataren Ƙungiyar Malaman Musulmai ta duniya.

Shugaban Ƙasar Aljeriya Abdelmadjid Tebboune ne ya buɗe masallacin, inda ya cika alƙawarin da ya yi na buɗe masallacin cikin yanayin farin ciki.

Duk da haka, taron ya kasance biki na musamman. Masallacin ya daɗe da buɗe ga masu yawon buɗe ido na ƙasa da ƙasa da maziyart zuwa Aljeriya tun kusan shekaru biyar da suka wuce. Amma an jinkirta bikin buɗewar da aka sha saka rana a baya.

Lokacin buɗe masallacin ga jama'a a hukumance ya zo daidai da bai wa mutane damar gudanar da sallolin dare a cikin watan Ramadan mai alfarma, wanda za a fara azumtarsa a wata mai zuwa.

Wani abin tarihi na jayayya da jinkiri

Wani kamfanin gine-gine na kasar China ne ya gina shi a tsawon shekarun 2010, babban masallacin Algiers yana ɗauke da hasumiya mafi tsayi a duniya, wadda ta kai ƙafa 869 (mita 265). Kudin aikin a hukumance shi ne dala miliyan 898.

Ɗakin yin sallar na masallaci na uku mafi girma a duniya baya ga Masallatai Biyu Masu Daraja na Makkah da Madina, yana ɗaukar mutum 120,000.

Zanensa na zamani ya ƙunshi al'adun Larabawa da Arewacin Afirka don girmama al'ada da al'adun Aljeriya da kuma filin saukar helikwafta da ɗakin karatu wanda zai iya ɗaukar littattafai har miliyan ɗaya.

Bayan girmansa, masallacin kuma kan yadda aka dinga samun tsaiko wajen buɗe shi da yin ce-ce-ku-cen da ya shafi shekaru bakwai da ake ginawa, ciki har da zaɓar wurin da za a yi shi, wanda masana suka yi gargaɗin cewa yana da haɗari.

Tun da farko dai masallacin wani aiki ne na tsohon shugaban ƙasar Abdelaziz Bouteflika, wanda ya tsara shi don ya zama mafi girma a Afirka. Ya so ya zama gadonsa kuma ya ba shi sun "Masallacin Abdelaziz Bouteflika" kamar Masallacin Hassan II a Casablanca, Maroko.

Wancan masallaci, wanda aka sanya wa sunan tsohon Sarkin Maroko - maƙwabciyar Aljeriya kuma abokiyar hamayyarta a yankin - an taɓa ayyana shi a matsayin mafi girma a Afirka.

Sai dai zanga-zangar da ta mamaye Aljeriya a shekarar 2019 da ta kai shi yin murabus bayan shafe shekaru 20 a kan karagar mulki, ta haramta wa Bouteflika aiwatar da shirinsa, wajen sanya wa masallacin sunansa ko kuma ƙaddamar da shi a watan Fabrairun 2019 kamar yadda aka tsara.

AP