Sabuwar dokar ta amince Ibrahim Traore ya tsaya takara a zaɓen da za a gudanar. /Hoto:Reuters

Gwamnatin mulkin soji ta Burkina Faso za ta ci gaba da mulki nan da shekaru biyar masu zuwa bayan mahalarta taro kan makomar ƙasar da aka yi ranar Asabar sun bayar da shawarar komawa kan mulkin dimokuraɗiyya zuwa watanni 60 daga watan Yuli mai kamawa.

Wannan shawara na cikin wata takarda da mahalarta taron suka amince da ita, wadda za ta kasance wani sabon tsari na gudanar da mulki a ƙasar.

Sojojin Burkina Faso sun ƙwace mulki a shekarar 2022 sannan suka yi alƙawarin gudanar da zaɓe a watan Yulin wannan shekarar domin komawa turbar dimokuraɗiyya, sai dai sun ce shawo kan rashin tsaron ƙasar shi ne babban abin da suka sanya a gaba.

Sabon tsarin, wanda shugaban mulkin sojin Burkina Faso Ibrahim Traore ya sanya wa hannu, ya nuna cewa za a mayar da mulki hannun gwamnatin farar-hula cikin watanni 60 daga ranar 2 ga watan Yuli.

"Za a gudanar da zaɓuka kafin wannan lokaci idan lamuran tsaro suka inganta," a cewar sabuwar dokar.

Sabuwar dokar ta amince Ibrahim Traore ya tsaya takara a zaɓen da za a gudanar.

Jinkirta lokacin gudanar da zaɓen yana iya sanya fargaba a zukatan masu rajin mulkin dimokuraɗiyya a Yammaci da Tsakiyar Afirka, inda aka gudanar da juyin mulki sau takwas a cikin shekaru huɗu da suka gabata.

Rashin tsaro na ci gaba da ƙarami a yankin Sahel na Yammacin Afirka irin su Burkina Faso, Mali da Nijar da ke makwabtaka da juna sakamakon hare-haren ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar-baya da ke da alaƙa da al Qaeda da Islamic State.

Burkina Faso ta yi fama da ƙaruwar hare-hare na ƙungiyoyin ta'adda a 2023, inda suka kashe sama da mutum 8,000, a cewar ƙungiyar ACLED da ke bin diddigin hare-haren 'yan ta'adda, mai mazauni a Amurka.

AFP