Ruwan da ya cika Kogin Tana ya wuce tsammani sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka tafka a Kenya. /Hoto: Reuters  

Wani jirgin ruwa dauke da akalla mutane 40 da ambaliyar ruwa ta rutsa da su ya kife a yankin kogin Tana na kasar Kenya a ranar Lahadi.

Hatsarin ya faru ne sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da ya haifar da ambaliya, inda ake fargabar mutane da dama ne suka mutu.

Kungiyar agaji ta Red Cross ta Kenya ta tabbatar da afkuwar lamarin cikin wata sanarwa da ta fitar tana mai cewa, ta bi sahun mutanen yankin wajen neman wadanda suka tsira daga haɗarin.

“An ceto mutane 23 kuma a halin yanzu suna samun kulawa a asibitin Madogo, yayin da wasu kuma ba a gansu ba,” in ji sanarwar.

Kogin Tana da ke yankin arewa maso gabashin Nairobi, babban birnin kasar, wanda ke da nisan kilomita 320 daga birnin, na cikin wuraren da ambaliyar ta fi shafa a yankin gabashin Afirka.

Sama da matsakaicin ruwan sama

Rahotannin sun bayyana cewa wani jirgin ruwa cike makil da mutane waɗanda suke kokarin neman mafaka daga yankunan da ambaliyar ruwan ta mamaye ne ya ci karo da ruwa mai gudu da ya yi sanadin aukuwar haɗarin.

Kazalika, hukumomi a Kenya sun tattabar da cewa akwai yiwuwar adadin mutanen da suka mutu sakamakon ambaliyar ya iya zarce mutum 90, inda suka yi gargadin cewa adadin ka iya karuwa saboda rahotannin da aka samu na bacewar wasu da dama a makon da ya gabata.

Kasar Kenya dai na fuskantar ruwan sama mai karfi da ke zuwa da hadari mai tsanani da yawan ruwan sama fiye da matsakaicin ''yawan ruwan'' da ake samu a lokacin damuna tsakanin watan Maris zuwa Mayu.

Yawan ƴan gudun hijira

Ma'aikatar hasashen yanayi ta kasar Kenya ta fitar da sanarwar gargadi inda ta bukaci jama'a da su yi shirin ko-ta-kwana don tunkarar ruwan sama mai karfin gaske nan gaba.

Ambaliyar ruwan da ake ci gaba da fuskanta ta mamaye kananan hukumomi 47, lamarin da ya haifar da ƙaurar mutane da dama daga matsugunansu, tare da lalata ababen more rayuwa da dukiyoyi da kuma haifar da asarar ruyuka.

A cewar gwamnatin Kenya, ambaliyar ta raba al'ummomi 24,196 waɗanda suka hada kusan mutane 131,450 da gidajensu, kana an kafa sansanoni 50 domin kula da ƴan gudun hijiran.

AA