APC ta zargi Atiku da nuna wa Tinubu ƙiyayya mai zafi. Hoto: OTHERS

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da ke mulkin Nijeriya ta yi zargin cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben 2023, Atiku Abubakar yana “matukar nuna ƙiyayya” ga shugaban kasar Bola Tinubu wanda yake gani shi ya hana shi yin nasarar zama shugaba a kasar.

APC ta bayyana haka ne a sanarwar da Sakataren watsa labaranta na kasa, Felix Morka, ya fitar ranar Alhamis jim kadan bayan tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi taron manema labarai kan takardun karatun Shugaba Tinubu, wadanda ya ce na bogi ne.

“Babban abin da ya fito fito fili a taron da ya yi a Cibiyar Yar’Adua Centre, musamman a wannan lokaci, shi ne Atiku yana matukar nuna ƙiyayya ga Tinubu, wanda yake gani shi ne yake da alhakin rashin nasara a zabukan shekarar 2007 da 2015 da 2019 da kuma wannan shekarar,” in ji APC.

Felix Morka ya ce a bayyane yake cewa a taron manema labaran, Atiku ɓaro-ɓaro ya nuna tashin hankalinsa, inda ya fayyace wasu daga cikin batutuwan da ke cikin ƙarar da ya ɗaukaka a Kotun Koli da kuma tuhume-tuhume marasa tushe da yake yi a kan Shugaba Bola Tinubu.

Taron manema labaran Atiku

Tun da fari a ranar Alhamis tsohon mataimakin shugaban kasar Nijeriyar Atiku Abubakar ya kira taron manema labarai a Abuja, inda ya bayyana cewa zai ci gaba da kalubalantar nasarar shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu, har sai Kotun Koli ta yanke hukuncin karshe.

Atiku ya ce tuni ma ya daukaka karar tasa da yake yi a kan Tinubu don “ceto dimokuradiyya. Kuma ba zan hakura da kalubalantar Tinubu ba har sai Kotun Koli ta yanke hukuncin ƙarshe,” ya ce.

Da aka tambaye shi ko ana matsa masa lamba don ya janye ƙarar, sai tsohon mataimakin shugaban Nijeriyar ya ce bayan zaben ya ji labarin cewa Shugaba Tinubu ya tura masa wata tawagar gwamnoni don tuntubarsa, “Amma ban ma bari sun zo gidana ba,” in ji Atikun.

Dan takarar shugaban kasar na PDP ya ce ana wani mataki na tabbatar da gaskiya da ɗa’a da sahihanci a al’amuran ƙasar.

Tuni bangaren Alhaji Atiku Abubakar ya ce ya tattara hujjoji 35 da yake so ya gabatar a gaban Kotun Kolin domin kalubalantar zaben Tinubu, amma babban makaminsa shi ne zargin cewa Shugaban Kasar ya yi amfani da takardar digiri ta bogi daga Jami’ar Jihar Chicago, da ya ce ya kammala a shekarar 1979, wanda hakan ya haifar da muhawara mai zafi a fagen siyasar kasar.

Sanarwar APC ta ƙara da cewa “Alhaji Atiku Abubakar shi ne mutumin da ya fi kowa tafka asara a fagen siyasar kasar kuma wanda ya fi kowa yawan tsayawa takarar shugaban Nijeriya a tarihi, kuma mun ga yadda a kwanan nan ya dage sai ya samo wata hujja daga Amurka a matsayin abun da ya kawo karshe burinsa na takarar shugaban kasa.

“A yayin da muke jajantawa Alhaji Atiku Abubakar kan tsawon lokacin da ya shafe yana son cimma wani buri da bai tabbata ba, muna yin tur da kakkausar murya kan hanyar da ya bi ta tona asirin Nijeriya da fadar shugaban kasa a kasar waje."

TRT Afrika