| hausa
AFIRKA
5 MINTI KARATU
Na gana da Tinubu a Faransa - Kwankwaso
A takaitacciyar hirar da ya yi da TRT Afrika, Sanata Kwankwaso, ya ce yanzu ba zai fadi gundarin abin da suka tattauna a kai ba, amma zai fayyace komai a ranar Alhamis.
Na gana da Tinubu a Faransa - Kwankwaso
Rabiu Musa Kwankwaso ya ce babban burinsa shi ne cigaban Nijeriya Hoto/Kwankwaso Twitter
16 Mayu 2023

Dan takarar shugaban Nijeriya a zaben 2023 a Jam'iyyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, ya tabbatar da cewa ya gana da shugaban kasar mai jiran gado Bola Ahmed Tinubu.

A takaitacciyar hirar da ya yi da TRT Afrika, Sanata Kwankwaso ya ce ba zai fadi gundarin abin da suka tattauna a kai ba sai ranar Alhamis mai zuwa.

An yi wannan ganawa ce a birnin Paris na kasar Faransa a ranar Talata.

Ga yadda hirarmu ta kasance da tsohon gwamnan jihar Kano:

Tambaya: An ce ka gana da shugaba mai jiran gado Bola Ahmed Tinubu, ko za mu iya sanin me kuka tattauna?

Kwankwaso: E, haka ne, amma ba zan yi karin bayani a yanzu ba. Sai ranar Alhamis za mu fitar da cikakken bayani.

Tambaya: To amma za a iya cewa ganawar wani abu ne da magoya baya da bangarorin biyu duka za su ji dadinta?

Kwankwaso: Ai mun soma yi kenan, ku bari a gama mana.

Tambaya: Hakan na nufin za ku shafe kwana uku kenan ana tattaunawar?

Kwankwaso: E, ku bari dai sai jibi ku kira ni a waya don karin bayani.

Wasu rahotanni sun nuna cewa tsohon gwamnan jihar Kano zai sauya sheka daga NNPP zuwa Jam'iyyar APC mai mulkin Nijeriya kuma zai taka muhimmiyar rawa a gwamnatin Bola Tinubu.

Wannan batu dai ya zama abin tattaunawa a kafafen watsa labarai da shafukan sada zumunta da majalisu har ma da teburan masu shayi a Nijeriya.

Jim kadan da bayyanar labarin ne mutune suka hau tattaunawa a kansa a Nijeriya, inda har ya zaman a farko mafi tashe a shafukan sada zumunta na kasar.

Rashin sanin ainihin abin da manyan 'yan siyasar biyu suka tattauna, duk da cewa wasu rahotanni sun ce sun shafe tsawon lokaci suna ganawar ta sirri, ya sa al’ummar Nijeriya sun kagu matuka don sanin me tattaunawar ta kunsa.

'Muna rokon Allah ya bai wa Abba Gida-Gida hikimar warware matsalar da aka shuka a Kano'

Tinubu da Kwankwaso sun fafata a zaben shugaban kasa da aka yi a watan Fabrairun bana, kuma duk da cewa adawa ta fi zafi ne tsakanin Tinubu na Jam’iyyar APC da Atiku Abubakar na PDP, a matakin jiha an ga yadda adawar ta yi zafi tsakanin bangaren Kwankwaso da APC karkashin Gwamna Abdullahi Ganduje, wanda ya tsayar da mataimakinsa Nasiru Gawuna a matsayin dan takara.

Mafi yawan wadanda suka yi ta tsokaci suna bayyana fatan ganin Kwankwaso ya koma jam’iyya mai mulki don mara wa sabuwar gwamnatin baya.

Abin da ‘yan Nijeriya ke cewa

Ga dai abin da wasu ke cewa:

Mai taimaka wa Shugaba Buhari kan harkokin shafukan sada zumunta BAshir Ahmad ya wallafa a Twitter cewa: "Tabbas muna bukatar Kwankwaso a jam'iyyarmu a Kano. Za mu yi farin cikin dawowarsa.

Muhsin Ibrahim ya ce "Na yi farin cikin jin cewa Tinubu da Kwankwaso sun gana. Ina fatan ganwar ta zama mai amfani. Kwankwaso yana da karsashi, kwararre ne kuma ya damu kwarai da Cigaban Nijeriya. Tabbas, bai kamata a sha wahalar shawo kansa don komawa cikin gwamnati ba - ba lallai sai APC ba."

Muhammadu Tijjani ya ce "Ba zan taba zargin Kwankwaso don ya hade da wani ba, jam'iyyarmu ce ta uzzura masa kuma ba ta ba shi girmansa da ya dace ba. Me ya sa kowa yake korafi yanzu? Siyasa fa ra'ayi ce kuma kowa muradunsa yake karewa."

Masu iya magana kan ce, "Wasa farin girki..." Abu na gaba shi ne jiran ranar Alhamis don jin yadda za ta kaya.

MAJIYA:TRT Afrika da abokan hulda
Rumbun Labarai
Ghana za ta tura injiniyoyin soji don taimakawa wajen sake gina Jamaica bayan afkuwar guguwa
Mutane 70 sun ɓace bayan jirgin ruwa ɗauke da mutum 120 ya kife a DRC
Wata ƙungiya ta zargi kamfanin Nestle da sayar wa Afirka abincin jarirai mai sikari da yawa
Ranar Makewayi ta Duniya: Kundin tsafta na Afirka don inganta lafiya da mutunci
Sabon Alƙalin Alƙalan Ghana Baffoe-Bonnie ya fara aiki
An raba fiye da mutum 100,000 da gidajensu a Al Fasher na Sudan daga lokacin da RSF ta ƙwace birnin
Kafafen watsa labaran Afirka: Abokan kawo ci gaba da ake mantawa da su
Za a ƙara farashin man fetur a Ghana
Ruftawar mahaƙar ma’adanai ta yi ajalin aƙalla mutum 32 a DRC
An samu rahotanni 32 na yi wa 'yan mata fyade bayan RSF ta ƙwace birnin Al Fasher - Likitoci
Mutum huɗu sun rasu bayan jiragen ruwa biyu na 'yan ci-rani sun kife a gaɓar tekun Libya
DR Congo da M23 sun cim ma yarjejeniyar zaman lafiya 'ta tarihi' a Qatar
AfDB zai ba Nijar CFA biliyan 98.7 domin magance matsalar ruwa ta shekara 70 a Zinder
MDD ta yi gargaɗi kan ƙazancewar yaƙin Sudan, ta yi kira kan barin shigar da kayan agaji
An gabatar da GH¢302bn a matsayin kasafin kuɗin Ghana na 2026 ga majalisar dokokin ƙasar
Sojojin Sudan sun daƙile harin RSF kan filin jirgin sama da dam a arewacin ƙasar
Rubio ya nemi a daina bai wa RSF makamai, ya ɗora wa rundunar laifi kan kashe-kashe a Al Fasher
Dalilin da ya sa TikTok ya goge bidiyoyi miliyan 1.5 da 'yan Uganda suka wallafa
Mutum 12 sun mutu a turmutsutsun neman aikin soja a Ghana – Rahotanni
Mahaucin Al Fasher: Yadda hotonsa ya zama alamar bakin cikin Sudan