Wata kotu a kasar Chadi ta bai wa shugaban mulkin soja Mahamat Idriss Deby damar tsayawa takara shugabancin ƙasar/Photo:Reuters

A ranar 6 ga watan Mayu ne za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa zagaye na farko a ƙasar Chadi, wanda zai kawo ƙarshen wa'adin miƙa mulki da aka kwashe shekaru uku ana yi, kamar yadda hukumar zaɓen ƙasar ta sanar a ranar Talata.

An ayyana Janar Mahamat Idriss Deby Itno a matsayin shugaban gwamnatin mulkin soja shekaru biyu da suka gabata bayan da 'yan tawaye suka kashe mahaifinsa, wanda ya mulki kasar tsawon shekara 30.

Mahamat Deby ya yi alkawarin miƙa mulki ga farar hula tare da shirya zaɓe cikin watanni 18 amma ya ƙara da wasu shekaru biyu na miƙa mulki.

An tura ƙarshen lokacin miƙa mulki zuwa 10 ga Oktoban 2024.

'Shari'a'

"Bayan wannan ranar, kasar za ta fada cikin wani hali na shari'a, mai kama da ruɗani da za a iya gani," in ji Ahmet Bartchiret, shugaban hukumar zaben ANGE.

"Don haka ya zama wajibi a gudanar da zaɓen tukuna."

A tsakiyar watan Janairu, ƙungiyar mahaifinsa ta Patriotic Salvation Movement (MPS) ta zaɓi Deby Itno a matsayin ɗan takararta na zaɓen shugaban ƙasa.

Deby ya shaida wa Ƙungiyar Tarayyar Afirka cewa ba zai tsaya takarar shugabancin ƙasar ba, amma sabon kundin tsarin mulkin da aka amince da shi a tsakiyar watan Disamba ya ba shi damar yin hakan.

TRT Afrika