Sojojin Nijeriya sun kashe ƴan ta'adda da dama a ƴan kwanakin nan. / Hoto: NA

A yayin da ake ci gaba da samun hare-haren ƴan bindiga da masu garkuwa da mutane a wasu sassa na arewacin Nijeriya, rundunar sojin ƙasar na bayyana irin nasarorin da take samu a yaƙin da take ci gaba da yi da ta’addanci a ƙasar.

Kusan kowane mako sojojin ƙasar na sanar da irin nasarorin da suke samu ta hanyar kai wa ƴan bindigan farmaki da harin ƙwanton-ɓauna da na ba-zata a maɓoyar ƴan bindigar.

Haka kuma jefi-jefi sojojin kan sanar da batun kashe kwamandoji ko kuma gawurtattun ƴan fashin daji waɗanda suka addabi al’ummomi daban-daban na arewacin ƙasar.

Ga wasu daga cikin gawurtattun ƴan fashin da sojojin suka kashe a ƴan kwanakin nan:

Ali Kacalla

A watan Disambar 2023 ne Rundunar Sojin Nijeriya ta tabbatar da kashe Ali Kacalla wanda aka fi sani da Ali Kawaje.

An kashe shi ne a Karamar Hukumar Munya da ke jihar Neja a lokacin da yake tare da mayaƙansa.

Ali Kachalla shi ne ɗan bindigar da ya yi garkuwa da dalibai na Jami’ar Tarayya da ke Gusau haka kuma rahotanni sun ce shi ne wanda ya harbo jirgin yaƙin sojin Nijeriya a kusa da ƙauyen Kabaru da ke yammacin Dan Sadau a Jihar Zamfara.

Yellow Jambros

Yellow Jambros na daga cikin ƴan ta’addan da suka addabi jihohin arewa maso yammacin Nijeriya da garkuwa da mutane.

Sojojin saman ƙasar ne suka kashe shi tare da gomman mayaƙansa a lokacin da jiragen yaƙi suka yi masu ruwan wuta a Karamar Hukumar Shiroro da ke Jihar Neja.

Mai magana da yawun sojojin saman na Nijeriya Edward Gabkwet ya ce Jambros na da hannu a garkuwa da mutane da kashe-kashe a hanyar Abuja zuwa Kaduna da wurare da dama a Kaduna da Katsina da Zamfara.

Boderi Isyaku

Boderi Isyaku shi ne na baya-bayan nan da jamia’n tsaron Nijeriya suka kashe bayan sun shafe shekaru suna nemansa.

Boderi ya shahara wurin kai hare-hare da garkuwa da mutane a yankunan Sabon Birni da Rigasa da Gwagwada da Rijana da Katari da kan hanyoyin Kaduna zuwa Abuja da kuma Kaduna zuwa Birnin Gwari da wasu yankuna na Jihar Neja.

Baya ga garkuwa da mutane, ya shahara wurin satar shanu da kuma dillancin makamai.

Boderi ne ya kitsa garkuwa da ɗaliban Kwalejin Gandun Daji da ke Afaka Kaduna a ranar 11 ga watan Maris ɗin 2021, kamar yadda Samuel Aruwan ya tabbatar, Kwamishinan Gudanarwa na Jihar Kaduna, kuma mai sa ido a Ma’aikatar Tsaro da Harkokin Cikin Gida ta jihar.

Haka kuma Boderi ne ya kitsa harin da aka kai a ranar 24 ga watan Agustan 2021 a kwalejin sojoji ta NDA da ke Afaka Kaduna inda har aka kashe sojoji biyu.

Bayan makonni da kai wannan harin ne Boderi ya jagoranci garkuwa da Sarkin Bungudu Alhaji Hassan Atto.

TRT Afrika