Hukumar hasashen yanayin ta bukaci da a kula sosai saboda yiwuwar samun ambaliya da kwarankwatsa. / Hoto: Reuters

Kenya da Tanzania na shirin fuskantar matsananciyar guguwa a lokacin da ake fuskantar mamakon ruwan sama da mummunar ambaliyar ruwa da suka damalmala Gabashin Afirka suka kuma yi ajalin sama da mutum 350 tare da tursasawa dubbai barin matsugunansu.

Baya ga janyo asarar rayuka 188 tun watan Maris a Kenya, ambaliyar ruwan ta raba mutum 165,000 da matsugunansu, an samu rahotannin ɓatan mutum 90, in ji Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida, inda gwamnati ta gargadi 'yan kasa da su kasance cikin halin kar ta kwana.

"Ana bayyana cewa akwai yiwuwar yankin da ke gabar teku ya fuskanci guguwar Hidaya, wadda za ta zo tare da mamakon ruwan sama, guguwa mai ƙarfi da za ta iya shafar harkokin teku a Tekun Indiya," in ji ofishin Shugaban Kasar Kenya William Ruto a ranar Alhamis.

A maƙwabciyar Tanzania da akalla mutane 155 suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwa da zaftarewar kasa, ana sa ran za a fuskanci guguwar ta Hidaya.

Mamakon ruwan sama a kwanaki masu zuwa

"Zuwan guguwar Hidaya na iya mamaye dukkan tsarin yanayi a kasar ciki har da mamakon ruwan sama da kakkarfar iska a yankunan da ke gaba da Tekun India," in ji Kungiyar Bayar da Agaji ta Red Cross a Tanzania a wata sanarwa ta shafin X.

Nairobi babban birnin Kenya na daga cikin yankunan da ake sa ran za su samu mamakon ruwan sama a kwanaki uku masu zuwa, in ji Sashen Kula da Yanayi na Kenya a sanarwar da ya fitar ta shafinsa na dandalin X, yana mai gargadin yiyuwar samun ƙaƙƙarfar guguwa a gabar tekun kasar.

Hukumar hasashen yanayin ta bukaci da a kula sosai saboda yiwuwar samun ambaliya da kwarankwatsa, tana mai kara wa da cewar ƙaƙƙarfar guguwar na iya tumbuke rufin kwanon gidaje da bishiyu da ma sauran barna.

Ruwan saman da ba a saba ganin irin sa ba ya janyo ambaliyar da ta yi ajalin mutum 29 da jikkatar wasu 175 a Burundi, wasu dubban kuma sun rasa matsugunansu tun watan Satumban bara, in ji Majalisar Dinkin Duniya.

Lamarin ya rutsa da 'yan yawon bude ido

A farkon makon nan ne Shugaban Kenya Ruto ya sanar da zai aike da sojoji su kwashe mutanen da ambaliyar ruwa ta rutsa da su.

A wata sanarwa da aka fitar a yammacin Alhamis, Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida ta umarci duk wanda ke zaune a kusa da manyan koguna ko madatsun ruwa da su bar yankunan cikin awanni 24, suna masu gargadin idan ba haka ba to komai zai iya faruwa.

Mummunan lamarin ya kuma shafi sashen yawon bude ido na Kenya -- babban sashen habaka tattalin arziki - inda lamarin ya rutsa da 'yan yawon bude ido 100 a Gandun Dajin Maasai Mara a ranar Laraba bayan kogi ya balle, ruwa ya mamaye matsugunan 'yan yawon bude ido.

Daga baya masu aikin ceto sun kwashe mutane 90 ta kasa da ta sama, in ji Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida.

Mummunar asara

Ba a iya isa ga yankin saboda gadoji sun karye, shugaban Narok West, Stephen Nakola ya fada wa AFP, yana mai kara wa da cewar lamarin ya shafi kusan wuraren da ‘yan yawon bude udo ke zune guda 50, inda sama da mutanen yankin 500 suka rasa ayyukan yi.

Babu asarar rayuka amma kuma jama’ar yankin sun bar matsugunansu.

Nakola ya kara da cewa “A yanzu da wahala a iya isa ga Mara, mutanen da suka makale a yankin an cikin damuwa, bas u da hanyar fita.”

“Na damu matuka kan yadda yanayin zai iya tsamari saboda har yanzu ana yin ruwan sama.”

A lamari daya da ya faru a Kenya, kauyawa da dama sun ras arayukansu a lokain da wata madatsar ruw ata karye a ranar Litinin a kusa da Mai Mahiu, a Wadin Rift, kilomita 60 nesa daga babban birnin Nairobi.

Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta ce an gano gawarwakin mutane 52, ana ci gaba da neman wasu 51 da suka bata.

Gargadin yin balaguro

‘Yan siyasa na jam’iyyun adawa da kungiyoyin fafutuka sun zargi gwamnatin Ruto da rashin yin shirin d aya kamata, kuma tana tafiya wahainiya wajen kai dauki ga yankunan da ibtila’in ya shafa.

Kungiyar Kare Hakkokin Dan Adam ta Human Rights Watch ta ce “Gwamnatin Kenya na da alhakin kare jama’a daga cutuwa da illar da ka iya zuwa sakamakon sauyin yanayi da tsananin guguwa da ruwan sama, dole ne ta kare jama’a.”

Amurka da Birtaniya sun bayar da gargadin tafiya zuwa Kenya ga ‘yan kasashensu, suna kiran ‘yan kasashen nasu da su kula sosai a wannan halii na munanar yanayi.

Bayan afkuwar lamarin, an dinga aikewa da sakon ta’aziyya da jaje ga Kenya, ciki har da ma Pope Francis da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres.

TRT Afrika da abokan hulda