Gwamna Abba Kabir ne ya bai wa Sarki Sanusi takardar naɗa shi sarki ranar Juma'a 24 ga watan Mayu, 2024 a Gidan Gwamnatin Kano. / Hoto: Masarutar Kano.

Gwamnan Kano da ke Nijeriya Alhaji Abba Kabir Yusuf ya bai wa Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II takardar kama aiki a matsayin Sarkin Kano.

Abba Kabir Yusuf ya bai wa sarkin takardar ne a Gidan Gwamnatin Kano ranar Juma’a, kwana ɗaya bayan Majalisar Dokokin jihar Kano ta amince da gyaran Dokar Masarautun jihar, sannan gwamnan ya sa mata hannu.

Sarki Sanusi ya shiga Kano ne a ranar Juma’a, inda ya samu tarba daga Hakimai da jami’an gwamnati da kuma wasu al’ummar Kano.

Miƙa masa takardar na nufin cewa a yanzu ya zama halastaccen Sarkin Kano, kuma a yanzu ya zama Sarki na 14 da kuma 16 a jerin sarakuna Fulani.

Gwamna Abba Kabir ne ya bai wa Sarki Sanusi takardar nada shi sarki ranar Juma'a 24 ga watan Yuni, 2024 a Gidan Gwamnatin Kano. / Hoto: Masarutar Kano.

Daga bisani, Sarki Sanusi II ya jagoranci gwamnan jihar da sauran al'umma wurin gudanar da sallah Juma'a a masallacin Gidan Gwamnati.

Sake naɗa shi Sarki ya sa ya kafa tarihi inda ya zama sarkin Fulani na farko da aka sauke sannan aka sake naɗa shi.

Sarki na farko shi ne shi ne Muhammadu Kukuna a Gidan Bagauda wanda aka sauke a 1652, sannan aka sake naɗa shi sarki a wannan shekarar.

A ranar Alhamis ne dai ɗaya daga manyan Hakiman Masarautar Kano Sarkin Dawaki Babba Alhaji Aminu Babba Ɗanagundi ya shigar da ƙara kotu yana neman a hana gwamnati aiki da sabuwar Dokar Masarautun.

To sai dai a lokacin da yake jawabi bayan bai wa Sarki Sanusi takarda, Gwamna Abba Kabir ya ce umarnin da aka karɓo daga kotu ya makara.

“Na kafa hujja da cewa na sa hannu a kan Dokar Masarautar Kano da ƙarfe biyar na yamma, amma sai karfe biyu na dare wani ya zo ya ce wai wannan abin bai yi ba,” a cewar gwamna Abba.

“Mun sa hannu karfe 5:20, wai alkalin ma da ya ba da odar wai yana Amurka wai ya ba mu oda.”

Ya ƙara da cewa “Idan kuma akwai lauya da zai ce mana abin da muka yi ba daidai ba ne, mu ma muna da namu lauyan da zai ce daidai ne.”

Gwamna Abba ya kuma yaba wa Majalisar Dokokin Jihar Kano kan gyaran Dokar Masarautun Kano, inda ta soke dokar da tsohuwar majalisa ta yi a lokacin Gwamna Ganduje, wacce ta ba da damar kafa masarautu biyar.

“Abin da majalisa ta yi shi ne ƙwato wa wanda aka cuta haƙƙinsa,” a cewar Abba Kabir.

Gwamna Abba ya ce doka ce ta ba su damar gyaran dokar, kuma sun yi abin da ya kamata.

“Saboda haka doka ta zauna a jihar Kano daram dam,” in ji Gwamna Abba.

“Idan al’ummar jihar Kano suka karɓa, to kowa ma ya je inda zai je, don mu al’ummar jihar Kano ne suka zaɓe mu.”

Ana jawabin, Sarki Sanusi II ya jinjina wa gwamnan Kano kan jajircewar da ya yi har ya mayar da shi kan sarauta da kuma kare martabar masarautar Kano.

Ana sa ran Sarki Sanusi zai shiga Gidan Sarautar Kano a makon gobe.

TRT Afrika