Band A su ne rukunin kwastomomi da suke samun wutar lantarki ta aƙalla awa ashirin a kowace rana./Hoto:Reuters

Gwamnatin Nijeriya ta ƙara kuɗin wutar lantarki ga rukunin kwastomomin da suka fi samun wuta, waɗanda ake kira Band A customers a turancin Ingilishi.

Band A su ne rukunin kwastomomi da suke samun wutar lantarki ta aƙalla awa ashirin a kowace rana.

A yayin da yake yi wa manema labarai jawabi a Abuja ranar Laraba, shugaban hukumar da ke sanya ido kan harkokin lantarki ta Nijeriya (NERC), Musliu Oseni ya ce yanzu kwastomomin za su riƙa biyan ₦225 kan kowane kilowat na wuta da suka sha maimakon ₦66 da suke biya a yanzu.

Oseni ya ce waɗannan kwastomomi su ne kashi 15 na mutum miliyan 12 da suke amfani da lantarki a faɗin Nijeriya.

Ya ƙara da cewa wannan sabon ƙarin kuɗin lantarki ba zai shafi sauran kwastomomi ba.

A watan Janairun da ya gabata, hukumar NERC ta ce gwamnatin Nijeriya za ta kashe kimanin N1.6 tr domin biyan tallafi kan kuɗin lantarki da za a bai wa ƴan ƙasar a shekarar 2024.

TRT Afrika