Hukumomi a Nijar na yawan kama masu safarar miyagun kwayoyi. Hoto/ActuNiger

Hukumar da ke yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Nijar, Octris, reshen jihar Maradi ta ce ta yi nasarar kama gawurtattun masu safarar kwayoyi a kasar.

Hukumar ta yi holen mutanen inda aka gabatar da kwayoyin Tramadol 49,600 wadanda aka kiyasta cewa sun kai CFA miliyan 27, kamar yadda jaridar ActuNiger ta ruwaito.

Hukumar ta ce an kai samamen a wani kango a birnin na Maradi inda aka kama mutanen.

A yayin samamen, ta kama mutum shida, daga ciki har da dan Nijeriya daya.

Insifecta Ali Dan Dijé, jagoran yanki na hukumar ta Octris, ya bayyana cewa dan Nijeriyar da aka kama dama sananne ne ga hukumar ‘yan sanda inda ya taba yi wa ‘yan sanda sojan-gona.

Hukumar ta Octris ta kara da cewa ta kama mota da babura uku wadanda ake amfani da su wurin safarar kwayoyin.

Mai shigar da kara, Mista Daouda Mamane, ya bayyana cewa masu safarar kwayoyin sun fito da wata hanya a yanzu inda suke amfani da babura domin bin wasu hanyoyi masu sarkakiya zuwa Maradi, inda daga nan ake kai kwayoyin arewacin kasar.

Ya bayyana cewa idan aka kai kwayoyin arewacin kasar ana ninka farashin sau hudu.

A ‘yan kwanakin nan hukumar ta Octris ta sha kama mutane kan zargin safarar miyagun kwayoyi.

Ko a watan nan sai da hukumar ta Octris ta kama wani gungu na masu safarar miyagun kwayoyi inda aka rutsa gungun a kan hanyarsa ta kai kwayoyi Libiya.

TRT Afrika